Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-03-07 21:59:29    
Kafofin watsa labaru na ketare sun mai da hankali sosai a kan rahoton gwamnati da Wen Jiabao ya yi

cri

Tun bayan da aka bude tarurrukan majalisu biyu, a ran 6 ga wata, wasu kafofin watsa labaru na ketare sun mai da hankali sosai a kan wadannan tarurrukan biyu da kuma rahoton kan ayyukan gwamnati da firayin ministan kasar Sin Wen Jiabao ya gabatar.

Jaridar Het Financieele Dagblad ta kasar Holland ta bayyana cewa, gwamnatin kasar Sin tana kara mai da hankali sosai a kan aikin samun bunkasuwa cikin dogon lokaci da rage gurbacewar muhalli, a sa'i daya kuma gwamnatin ta jaddada matsayinta a kan rage gibin da ke tsakanin matalauta da masu sukuni da kiyaye adalci.

Jaridar Ottawa Citizen ta kasar Canada ta ce, rahoton ayyukan gwamnati ya bayyana cewa, jam'iyyar kwaminis ta Sin za ta kara yaki da cin hanci da rashawa, kuma za ta kara zuba makudan kudi a kan aikin ilmi da kiwon lafiya, lallai wannan zai samu maraba daga jama'a.

Ban da wannan kuma, kafofin watsa labaru na kasar Amurka da Romania da Jamus da Rasha da kuma Britaniya da dai sauransu su ma sun mai da hankali sosai a kan tarurrukan majalisu biyu da kuma rahoton ayyukan gwamnati da firayin ministan kasar Sin Wen Jiabao ya gabatar da shi.(Danladi)