Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-03-07 21:56:43    
Shugabanin kasar Sin sun halarci tattaunawar da 'yan majalisu biyu na Sin suka yi

cri

Yau ranar 7 ga wata, shugabannin kasar Sin Mr. Hu Jintao, da Mr. Wu Bangguo, da kuma Mr. Wen Jiabao sun kai ziyara ga wakilan da ke halartar cikekken zama na biyar, wato taron shekara-shekara na majalisar ba da shawara kan harkokin siyasa ta kasar Sin, da kuma wakilan da ke halartar taron shekara-shekara na majalisar wakilan jama'r duk kasar Sin, kuma sun halarci tattaunawar da suka yi, inda suka saurari ra'ayoyi da shawarwari da 'yan majalisar suka gabatar kan manyan manufofi, da matsalolin da ke jawo hankulan jama'a sosai.

A gun taron da kungyiyar kwadago, da kungiyar matasa 'yan kwaminis, da kungiyar tarayyar mata da ta samari suka yi tare, 'yan majalisar ba da shawara sun sa himma domin ba da shawarwari. Shugaba Hu Jintao na kasar Sin ya yi wani muhimmin jawabi kan batun yadda ake raya zaman al'umma mai jituwa na gurguzu.

Shugaba Hu Jintao ya ce, gwamnatin Sin za ta yi iyakacin kokari kan tabbatar da kiyaye da kuma bunkasa babbar moriyar jama'a, a raya zaman al'umma mai jituwa da cin moriyarsa a yayin da ake raya zaman al'umma mai jituwa.

Shugaban majalisar wakilan jama'ar kasar Wu Bangguo ta kasar Sin, da firayin minista Wen Jiabao na kasar kuma, sun saurari jawaban da kungiyoyin wakilan Hongkong, da Mecau, da kuma jihar Hebei suka yi daya bayan daya. (Bilkisu)