Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-03-07 18:57:12    
Me ya sa kasashen Habasha da Eritrea sun yi cacar baki kan al'amarin garkuwa da aka yi wa masu yawon shakatawa

cri

A kwanakin baya ne aka yi garkuwa da rukunai guda biyu na masu yawon shakatawa na kasashen Turai a arewacin kasar Habasha. Daga baya kasar Habasha ta zargi kasar Eritrea da hannu a cikin wannan al'amarin garkuwar, amma kasar Eritrea ta musunta haka da babbar murya. Game da haka, wakiliyar gidan rediyonmu ta yi hira da Mr. Wang Hongyi, wani kwarara kan harkokin kudancin Asiya da Gabas ta tsakiya da na Afirka na gidan nazarin batutuwan duniya na kasar Sin. Ya ce, kasashen Habasha da Eritrea suna zargin juna kan al'amarin garkuwa, wannan ya nuna halin rashin tabbas da kuriyar Afrika ke ciki\. Indan ana son a gane dalilin da ya sa kasashen nan biyu suke cacar baki, da farko, ya kamata a dudduba tarihinsu, musamman ma rikicin da ke tsakaninsu cikin dogon lokaci.

"Kasashen Habasha da Eritrea kasa daya a tarihi, a karshen karni na 19, yankin Eritrea yana karkashin mallakar kasar Italiya. Daga baya, kasar Habasha ta hada kanta da Eritrea a shekaru 50 na karni na 20 bisa tsarin tarraya. Amma a shekarar 1962, kasar Habasha ta mai da Eritrea a matsayin wata jiha da karfi, jama'ar Eritrea ba su jin dadi da ganin haka, wannan ya haifar da yaki da makamai cikin dogon lokaci."

Mr. Wang Hongyi ya ce, a shekarar 1991, gwamnatin soja ta kasar Habasha ta fadi, saboda Eritrea ta taka muhimmiyar rawa wajen hamburar da gwamnatin soja, sabuwar gwamnatin kasar Habasha ta yarda da a kada kuri'ar raba gardama a Eritrea, jama'ar Eritrea sun zabi hanyar zaman kansu. Bayan Eritrea ta sami 'yanci, kasashen biyu suna rike da kyakkaawar hulda. Amma, 'yancin kasar Eritrea ya kawo wa kasar Habasha mugun tasiri wajen tattalin arziki.

"Ga Habasha, da farko, ta rasa wani yanki mai fadi. Na biyu, ta rasa mafita teku, Habasha tana dogara kan Eritrea wajen ciniki. Eritrea da Habasha, kasashe ne masu talauci a duniya, Eritrea ba ta yi amfani da kudin Habasha, ta yi amfani da dolar Amurka, wannan ya jawo hassara ga Habasha wajen tattalin arziki. Daga nan dangantaka da ke tsakaninsu ta fara lalacewa. Haka kuma zuwa shekarar 1998, an fara yaki da makamai tsakaninsu."

Mutane fiye da dubu 70 sun mutu a sakamakon wannan yaki, kuma mutane miliyoyi sun rasa gidajensu. Har zuwa shekarar 2000, bangarorin biyu sun daddale wata yarjejeniyar zaman lafiya. Amma Mr. Wang Hongyi yana ganin cwea, yarjejeniyar ba ta warware matsalar da ke cikin huldar tsakaninsu ba. A kan sami tashin hankali a yankunan dab da iyakar kasa tsakaninsu, musammam ma a wuri da masu yawon shakawata na kasashen Turai suka bace, wuri ne da bangarorin biyu suka taba yin yaki.

"Kamar yadda kowa ya sani, a shekarar 2006, jayayya da ke tsakaninsu ta kara tsananta, da farko, sun kori mutanen kiyaye zaman lafiya, na biyu, a kan maganar Somaliya, bangarorin biyu ko wanensu ya daure gindi ga wani rukuni daban, a karshe dai bangaren da kasar Habasha ta goyon baya ya ci, ammam halin da ke cikin wurin ba ya da kayu. Shi ya sa, an yi garkuwa da masu yawon shakatawa, wannan ba abin mamaki ba ne."

Mr. Wang Hongyi yana ganin cewa, kasashen biyu suna da sabanin ra'ayi kan maganar Somaliya, kuma yanzu suna yin cacar baki kan al'amarin garkuwa, wannan ya shaida rikicin da ke tsakaninsu.

"Duk tattalin arziki na kasashen biyu ba su da karfi, suna jin tsoron yin aikin soja kai tsaye, dalili kuma shi ne hassara da yakin ya kawo ba ta bace ba. har zuwa yanzu dangantaka tsakaninsu ba ta daidaitu, kan shafa iyakar kasa, kotun duniya ta Hague ta yanke shawarwari, amma Habasha ba ta aikata, Eritrea ta nuna rashin jin dadi ga zamantakewar duniya."

Mr. Wang Hongyi ya ce, da akwai shakka mai yawa kan batun garkuwa da aka yi kwannan baya, idan ba a daidaita wannan batu yadda ya kamata, sabanin da ke tsakaninsu zai kara tsanani.

"Da farko, a kafa huldar amincewa tsakanin shugabanni, da jam'iyyun kasashen biyu. Na biyu, bunkasuwa tare a kan tattalin arziki, saboda kasar Habasha ba ta da tashar jiragen teku, ta yi cinikin fici da shigi ta kasar Eritrea. Kasar Eritrea fa, tana rashin makamashi, kuma rashin karfin kawo al'barka. Saboda haka, idan kasashen biyu su kafa amincewa kan siyasa, kuma moriyar juna a kan tattalin arziki, za a warware matsalolin da ke tsakaninsu a zahiri."