Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-03-07 18:42:58    
Da kyar kasar Sin ke samun ci gaba wajen tsimin makamashi da sauran albarkatun kasa

cri
Yanzu, a nan birnin Beijing, majalisar wakilan jama'ar kasar Sin wato hukumar koli ta kasar tana zaman taronsa. Tsimin makamashi da sauran albarkatun kasa yana daya daga cikin muhimman abubuwa da Mr Wen Jiabao, firayim ministan kasar Sin ya bayyana, a cikin rahoto kan ayyukan gwamnati da ya gabatar a gun taron nan. Mr Wen Jiabao ya jaddada cewa, nan gaba kasar Sin za ta dauki matakai daban daban, wajen neman cim ma manufarta game da rage makamashi da take amfani wajen samar da kayayyaki a gida wato GDP. Bisa manufar nan, zuwa shekarar 2010, yawan makamashin zai ragu da kashi 20 cikin dari bisa na shekarar 2005.

A karamin yanki mai suna "Zhichunli" na unguwar Haidian ta birnin Beijing, mazauna suna kokari sosai wajen tsimin makamashi kuma ba tare da gurbata muhalli ba ta hanyar zaman rayuwarsu. Malam Li Chengfu wanda ke zama a wannan karamin yanki ya gabatar da shawararsa cewa, ya kamata, jama'a su rage tuka motoci masu zaman kansu, su kara daukar bus da sauran abubuwan hawa na jama'a. Ya kara da cewa, "dole ne, jama'a suna jin dadin tukar motocinsu, amma don tsimin makamashi da rage cunkuson motoci a kan hanyoyi, kamata ya yi, a sa kaimi ga jama'a da su dauki bus da sauran abubuwan hawa na jama'a. "

Wannan shawara shawara ce mai kyau ga tsimin man fetur da ake bukata. A kasar Sin, a karo na farko, yawan makamashi da aka yi amfani da shi wajen samar da kayayyaki wato GDP ya ragu a shekarar bara. Amma kasar ba ta cim ma manufarta dangane da rage kashi 4 cikin dari na makamashi da aka yi tsiminsu a shekarar bara ba. Da firayim minista Wen Jiabao ya tabo magana a kan dalilan da suka sa haka, sai ya bayyana a cikin rahotonsa cewa, "ana kyautata tsarin masana'antu sannu sannu, musamman manyan masana'antu wadanda ke cin makamashi mafi yawa kuma tare da gurbata muhalli sun karu ba yadda ya kamata ba, sa'an nan masana'antu da dama wadanda ke baya-baya wajen samar da kayayyaki, ba a rufe su yadda ya kamata ba. Wasu wurare da masana'antu ba su aiwatar da dokoki kan tsimin makamashi da kare muhalli a tsanake ba, kuma ana bukatar wani tsawon lokaci don samun sakamako mai kyau wajen aiwatar da manufofi da matakai da aka dauka."

Yanzu, masana'antu da yawa wadanda ke amfani da makamashi mafi yawa sun fara neman samun bunkasuwa ta hanyar zamani. Babban kamfanin narke karfe na birnin Kunming na lardin Yunnan da ke a kudu maso yammacin kasar Sin, a da, yawan kudi da ya kan kashe domin makamashi ya kai kashi 30 cikin dari na jimlar kudi da ya kashe wajen samar da kayayyaki, Malam Dou Yongping, babban injiniyi na kamfanin ya ce, tun bayan shekarar bara, kamfaninsa ya sami sakamako mai kyau wajen tsimin makamashi da sauransu. Ya ce, "na farko, a tsara manufofi game da tsimin makamashi, na biyu, a aiwatar da matakai da aka dauka wajen kyautata harkokin masana'antu a fannin fasaha. A yayin da kamfaninmu ke yin haka, yawan kudin da ya kashe wajen makamashi ya ragu da kudin Sin Renminbi Yuan miliyan 40 a ko wace shekara."

Yanzu, yawan makamashi da masana'antun kasar Sin ke ci ya dauki kashi 70 cikin dari bisa na duk makamashi da ake ci a kasar Sin. Da Malam Chen Shanru, shugaban hukumar kula da harkokin bunkasuwa da gyare-gyare ta lardin Guangdong da ke a kudancin kasar Sin ya ce, "lardinsa yana kokari sosai wajen bunkasa harkokin hidima da na jigilar kayayyaki da sauransu, ta haka zai iya tsimin makamashi sosai. Yawan kudin da muka samu daga wadannan harkoki ya kai kashi 42.2 cikin dari bisa na GDP a lardin. Idan an kwatanta su da na aikin masana'antu, yawan makamashi da aka yi amfani da shi wajen gudanar da harkokin nan ya kai kashi 20 cikin dari kawai bisa na aikin masana'antu." (Halilu)