Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-03-07 18:37:18    
Sin za ta kara karfin rage amfani da makamashi da kuma rage fitar da abubuwan gurbata muhalli

cri
Yau a nan birnin Beijing, shugaban kwamitin kula da harkokin bunkasuwa da gyare-gyare na kasar Sin, Mr.Ma Kai ya bayyana cewa, a shekarar da muke ciki, Sin za ta ci gaba da kara karfin rage amfani da makamashi da kuma rage fitar da abubuwan gurbata muhalli.

A gun taron manema labaru da aka shirya dangane da taron shekara shekara na NPC, Mr.Ma Kai ya ce, sakamakon tarnakin da makamashi da albarkatun kasa suka yi mata ne, tilas ne Sin ta kama hanyar raya zaman al'umma mai tsimin albarkatu wanda kuma ke da yanayi mai kyau.

Mr.Ma Kai ya kuma jaddada cewa, za a tsaya tsayin daka a kan cimma burin nan da gwamnatin Sin ta gabatar dangane da "rage yawan makamashin da ake kashewa a cikin ko wane GDP da kimanin kashi 20% cikin shekaru biyar, wato daga shekarar 2006 zuwa 2010, da kuma rage fitar da muhimman abubuwan gurbata muhalli da kashi 10%".(Lubabatu)