Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-03-07 17:24:57    
Musulmin kasar Sin

cri

Tambayar da za mu amsa a wannan mako ta fito ne daga hannun malam Sanusi Isah Dankaba, mazaunin birnin Keffi a jihar Nassarawa, tarayyar Nijeriya. Malam Sanusi Isa Dankaba, mai sauraronmu ne a kullum, kuma ya sha aiko mana wasiku tare kuma da yi mana tambayoyi. To, a cikin shirinmu na yau, za mu amsa wata tambayar da ya yi mana. A cikin wasikar da ya rubuto mana, ya ce, shin ko gaske ne a jihar Ningxia ta kabilar Hui mai ikon tafiyar da harkokin kanta, akwai musulmi masu yawa?

Masu sauraro, musulunci ya sami shigowa a nan kasar Sin ne a lokacin daulolin Tang da Song na gargajiyar kasar Sin, wato a kimanin karni na 7 zuwa karni na 13, kuma daga baya, ya yi ta bunkasa. Tun bayan zamanin daular Yuan kuma, musulunci ya bunkasa har ya zama wani addini mai zaman kanta kamar sauran addinai a kasar Sin. A nan kasar Sin, yawancin 'yan kabilun Hui da Uygur da Tartar da Kirgiz da Kazak da Uzbek da Dongxiang da Sara da Baoan wadanda yawansu ya kai sama da miliyan 18, suna bin musulunci. Musulmin kasar Sin sun fi zama ne a jihar Xinjiang mai ikon tafiyar da harkokin kanta ta kabilar Uygur da jihar Ningxia mai ikon tafiyar da harkokin kanta ta kabilar Hui da lardunan Gansu da Qinghai da Yunnan da dai sauransu. A halin yanzu dai, akwai masallatai fiye da dubu 30 a kasar Sin, kuma yawan limamai ya wuce dubu 40.

Masu sauraro, mun dai yi muku dan bayani a kan musulmin da ke nan kasar Sin. To, yanzu, bari mu koma kan tambayar da malam Sanusi Isa Dankaba ya yi mana, wato ko da gaske ne a jihar Ningxia akwai musulmai masu yawa. E, gaskiya ne haka yake. Ningxia jiha ce mai ikon tafiyar da harkokin kanta ta kabilar Hui. Asalin 'yan kabilar Hui ta kasar Sin zuriyoyi ne na 'yan kasuwa Larabawa da 'yan Farisa da suka zo kasar Sin a karni na 7 domin ciniki. A karni na 13, musulmi masu dimbin yawa sun shigo kasar Sin daga yankunan tsakiyar Asiya, kuma sun yi ta haduwa da 'yan kabilar Han da Uygur da Mongoliya da ke kasar, har ma sannu a hankali an fito da wata sabuwar kabila, wato kabilar Hui. 'Yan kabilar Hui suna amfani da harshen Sinanci a matsayin yarensu, a yayin da suka kuma yi amfani da wasu kalmomin Larabci da na yaren Farisa. 'Yan kabilar Hui suna biyayya ga musulunci. Bisa kidayar jama'a da aka yi kasar Sin a karo na biyar a shekarar 2000, yawan 'yan kabilar Hui ya kai fiye da miliyan 9 da dubu 816, har ma kabilar Hui ta zamanto ta uku a tsakanin kananan kabilun kasar Sin 55 a wajen yawan jama'a. 'Yan kabilar Hui suna zama ne a jihar Ningxia da lardunan Gansu da Qinghai da Henan da Xinjiang da Yunnan da Hebei da Anhui da Liaoning da Jilin da Shandong da kuma birnin Beijing. Amma a jihar Ningxia, an fi samun 'yan kabilar Hui. Ya zuwa karshen watan Faburairu na shekara ta 2006 da ta gabata, yawan 'yan kabilar Hui da ke zaune a jihar Ningxia ya kai kimanin miliyan 2 da dubu 100, wanda ya dau kashi 35.13% na yawan jama'ar Ningxia gaba daya. A jihar Ningxia, akwai masallatai sama da 3000, wadanda suka fito da yanayin musulunci sosai a nan lardin, sabo da haka, ana kiran jihar Ningixia jiha ce ta musulmi a kasar Sin.

Bayan da aka kafa jamhuriyar jama'ar Sin, an kuma kafa kungiyar kula da harkokin musulunci a nan kasar Sin, daga nan, addinin musulunci ya kara bunkasa a kasar Sin. Bayan da Sin ta aiwatar da manufar gyare-gyare da bude kofa ga kasashen waje, an nuna cikakkiyar girmamawa ga musulmai 'yan kabilu daban daban na kasar Sin, musulunci yana bunkasa cikin wani kyakkyawan yanayi a fannoni daban daban.(Lubabatu)