Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-03-07 13:49:16    
Beijing ta share faga ga karbar masu yawon shakatawa a lokacin ake yin taron wasannin Olympic na shekarar 2008

cri
An kiyasta cewa, a lokacin da ake yin taron wasannin Olympic a nan Beijng a shekara ta 2008, birnin Beijing zai karbi mutanen da yawansu zai kai dubu dari 6, wadanda za su hada da 'yan wasa da jami'an kula da gasanni na kasashen duniya da kuma mutanen ketare da za su zo nan don kallon taron wasannin Olympic. Yanzu masu aikin yawon shakatawa na Beijing suna share fage ga ayyukan karbar masu yawon shakatwa a lokacin da ake yin taron wasannin Olympic.

Bisa alkawarin da birnin Beijing ya yi a yayin da yake neman samun damar shirya taron wasannin Olympic, an ce, birnin Beijing zai gabatar da otel-otel masu taurari guda 800 domin taron wasannin Olympic, amma yanzu akwai irin wadannan otel guda 700 kawai a nan. A lokacin da take zantawa da wakilinmu, mataimakiyar shugaban hukumar yawon shakatawa ta Beijing madam Xiong Yumei ta bayyana cewa, birnin Beijing zai yi kwaskwarima kan otel-otel na yanzu a maimakon gina sabbin otel masu taurari. Ta yi karin haske cewa, Beijing za ta kara yi wa otel-otel misalin 4000 kwaskwarima don sanya wasu daga cikinsu su shiga cikin jerin otel-otel masu taurari. Zai cika alkawarin da ya yi a wannan fanni a karshen wannan shekara. Ta ce,'Yanzu mun kiyasta cewa, a lokacin da ake yin taron wasannin Olympic, Beijing za ta karbi 'yan kallo da masu yawon shakatawa da yawa, bisa halin da take ciki a fannin samar da masaukai, a galibi dai Beijing za ta biya bukatunsu. Yanzu muna bukatar kara kyautata matsayinmu na ba da hidima, musamman ma a cikin otel marasa taurari. Za mu mai da hankali kan wannan aiki a shekarar da muke ciki.'

Madam Xiong ta kara da cewa, birnin Beijing zai ci gaba da daga matsayin masana'antun samar da masaukai wajen ba da hidima, zai ci gaba da ayyukan neman dakuna a lokacin taron wasannin Olympic da bunkasa na'urori marasa shinge a otel-otel, sa'an nan kuma, zai horar da ma'aikatan otel da ilmin wasannin Olympic da ladabi da harsunan waje.

A yayin da yake karfafa karfinsa na karbar baki, birnin Beijing zai dora muhimmanci kan gyare-gyaren da masana'antun otel suke yi a fannin kiyaye muhalli. Yanzu hukumar yawon shakatawa ta Beijing tana aiwatar da ma'aunin kiyaye muhalli da lafiyar mutane a otel-otel 122 da suka daddale yarjejeniya tare da kwamitin shirya taron wasannin Olympic na Beijing, kuma za su karbi bakin ketare a lokacin taron wasannin Olympic. An bukaci wadannan otel-otel da su ba da dakuna da abinci masu lafiya da suka dace, wadanda suka biya bukatu a fannin kare muhalli, a sa'i daya kuma, za su kiyaye muhalli da yin amfani da albarkatu yadda ya kamata. Ban da wannan kuma, an riga an soma dudduba su ta fuskar kiyaye muhalli a hukunce.

Beijing International Hotel na daya daga cikin irin wadannan otel, babban darektansa Chen Xuhua ya gabatar da cewa, yanzu otel dinsa ya zuba kudin Sin yuan miliyan 5 zuwa 6 wajen yin kwaskwarima kan ayyukansa na yanzu, ya kuma dauki matakai da dama don yin tsimin makamashi da kiyaye muhalli. Ya ce,'Yanzu muna namijin kokarin sake yin amfani da kayayyakin dakuna don kiyaye muhalli. Bakinmu da mu za mu taimaka wa juna, ko wane bako zai yi amfani da zanen gado kafin ya tashi daga otel, a maimakon wanke su a ko wace rana, ta haka za a rage bata da gurbata ruwa. Haka zalika kuma, mun yi kokarin rage yawan kayayyakin da a kan yi amfani da su sau daya kawai. Sa'an nan kuma, muna daukar wasu matakai don yin tsimin wutar lantarki da ruwa.'

Yanzu wasu 52 daga cikin dukan wadannan otel-otel 122 sun zartas da kimantawar da aka yi musu. An ce, tun daga watanni 6 na karshe na wannan shekara, kwamitin shirya taron wasannin Olympic na Beijing zai hada kansa da masanan hukumomin da abin ya shafa su don dudduba dukan otel-otel da za su karbi bakin ketare a fannin kiyaye muhalli, idan ba su amince da abun da suka gani ba, za a soke izninsu na karbar bakin ketare a lokacin taron wasannin Olympic na Beijing na shekara ta 2008.

Akwai wani labari daban da aka samu, an ce, otel-otel wadanda za su karbi bakin ketare a lokacin taron wasannin Olympic na shekara ta 2008 sun riga sun tabbatar da farashin dakuna, an kara farashin dakuna na yanzu kadan, amma yawan karuwar farashin ya yi kasa da na lokacin taron wasannin Olympic na Sydney da Athens. Ban da wannan kuma, mutane suna iya fara neman dakuna a masaukan da suka hada da masaukin matasa da dai sauransu na Beijing ta yanar gizo domin samun wuraren kwana a lokacin da ake yin taron wasannin Olympic na Beijing na shekara ta 2008, za su sami fifiko kadan.(Tasallah)