Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-03-07 13:48:02    
Wasu labaru game da wasannin motsa jiki(01/03-07/03)

cri
Bisa sabuwar kididdigar da sashen kula da harkokin masu aikin sa kai na kwamitin shirya taron wasannin Olympic na Beijing ya samu, an ce, tun da aka fara daukar masu aikin sa kai domin taron wasannin Olympic na Beijing da na nakasassu a ran 28 ga watan Agusta na shekarar bara, har zuwa karshen watan Fabrairu na shekarar nan da muke ciki, jimlar mutanen da suka yi rajista ta wuce 350,000, wadda ta fi jimlar masu aikin sa kai da ake bukata, wato 100,000. Wani jami'in kwamitin ya bayyana cewa, mutanen da ba su samu damar zama masu aikin sa kai a cikin gasanni ba za su iya gudanar da ayyukan sa kai a fannonin harkokin birane da zaman al'ummar kasa, za a soma daukar irin wadannan masu aikin sa kai tun daga watan Yuni na shekarar bana.

A kwanan baya, wani jami'in hukumar wasannin motsa jiki ta kasar Sin ya sanar da cewa, a shekarar 2006 da ta gabata, kasar Sin ta aiwatar da ayyukan wasannin motsa jiki fiye da 26,000 domin 'yan kauyuka, wadanda suka kashe kudin Sin yuan biliyan 1.1. Tun can da, ana fama da karancin muhimman ayyukan wasannin motsa jiki a kauyukan kasar Sin, amma tun da shekarar bara, gwamnatin Sin ta kara raya ayyukan wasannin motsa jiki a kauyuka, ta kuma yi kokari domin ganin cewa, za a sami filayen wasa na al'umma a kauyukan kasar da yawansu ya kai kashi daya cikin kashi 6 a shekara ta 2010.

Ran 3 ga wata, 'yar wasa Xie Xingfang ta kasar Sin ta zama zakara a cikin gasa ta tsakanin mace da mace ta budaddiyar gasar wasan kwallon badminton da aka yi a kasar Jamus, ta kuma sami kyautar kudi da yawansa ya kai dalar Amurka 80,000. A sakamakon haka, kungiyar kasar Sin ta samu lambobin zinariya 4 a cikin gasa ta tsakanin namiji da namiji da tsakanin mace da mace da tsakanin mata biyu biyu da kuma gasar gaurayawar namiji da mace.

Ran 27 ga watan Fabrairu, an sanar da sunayen 'yan takarar neman samun lambar girmamawa ta wasannin motsa jiki ta duniya ta Laureus ta shekara ta 2007, 'yar wasan kwallon kafa Ma Xiaoxu ta kasar Sin mai shekaru 18 da haihuwa ta shiga wannan takardar sunaye a matsayin sabuwar 'yar wasa mafi nagarta. An mayar da Ma Xiaoxu tamkar sabuwar tauraruwa a rukunin wasan kwallon kafa na mata na duniya. (Tasallah)