Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-03-06 20:56:07    
Dakin tunawa da Jiaxuan

cri

Barkanmu da sake saduwa da ku a cikin shirinmu na yawon shakatawa a kasar Sin, wanda mu kan gabatar muku a ko wace ranar Talata. A cikin shirinmu na yau, kamar yadda mu kan yi a da, da farko za mu karanta muku wasu abubuwa kan dakin tunawa da Jiaxuan, wanda shahararren mawaki ne kuma jarumi na al'ummar kasar Sin, daga baya kuma, za mu maimaita shirinmu na musamman na gasar kacici-kacici ta 'garin Panda, lardin Sichuan', za mu sake karanta muku bayanin musamman mai lakabi haka 'babban dutse na Qingchengshan da kuma madatsar ruwa ta Dujiangyan'.(music)

An gina dakin tunawa da Xin Qiji ne don nuna masa girmamawa, wanda aka haife shi a shekara ta 1140 bayan haihuwar Annabi Isa A.S., ya mutu a shekara ta 1207, shi ne shahararren mawaki, kuma jarumin al'ummomin kasar Sin na zamanin daular Nansong.

Wannan dakin tunawa daki ne da aka gina bisa salon gine-gine na gargajiya na kasar Sin sosai. Ya kasance da wani allo a kan babban kofarsa, inda mashal Chen Yi na kasar Sin ya rubuta manyan kalmomi 6 na Sinanci masu launin zinariya, wadanda ma'anarsu ita ce dakin tunawa da Xin Qiji.

Xin Qiji, wanda ake yi wa da lakabi da Jiaxuan, ya zo daga birnin Jinan. A lokacin da aka haife shi a shekara ta 1120, sojojin daular Jin sun mamaye duk kasarsa, kuma gwamnatin daular Beisong na bakin tarwatsewa. Xin Qiji ya tattara sojoji a birnin Jinan ya sha yin gwagwarmaya da abokan gaba a lokacin da shekarunsa ya kai 21. Wata rana sojojin daular Jin sun shirya wata liyafa, Xin shi kadai ne ya shiga cikin sananinsu kan wani doki, ya kama dan tawaye wai shi Zhang Anguo da rai don mayar da martani dangane da rasuwar janar daular Beisong mai suna Geng Jing.

Xin Qiji ba kawai wani jarumin al'ummar kasar Sin ne wanda ke kishin kasarsa sosai ba, har ma wani mawaki ne kuma tsohon dan siyasa. A cikin dakin tunawa da shi, an ajiye hotunsa da bayanin tarihinsa da kuma muhimman takardun da masu baya da shi suka rubuta game da shi da kuma wakokinsa. A cikin bangarori 2 na babban zauren, ana nuna jerin muhimman abubuwan da suka faru a cikin lokacin ran Xin da adawali da zane-zane kan ayyukan da ya yi da kuma hotunan da aka dauka a garinsa da tsohon dakin da ya taba zama da kuma kabarinsa.