Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-03-06 20:47:50    
Hanyar zaman rayuwa ta kiwon lafiya za ta ba da taimako wajen magance ciwon toshewar jijiyoyin jini na zuciya da na kwakwalwa

cri

Barkanmu da sake saduwa a wannan fili mai farin jini wato "kimiyya da ilmi da kuma kiwon lafiya na kasar Sin". A cikin shirinmu na yau, da farko za mu yi muku da bayani kan cewa, hanyar zaman rayuwa ta kiwon lafiya za ta ba da taimako wajen magance ciwon toshewar jijiyar zuciya da ta kwakwalwa, daga baya kuma za mu karanta muku wani bayani kan ranar karanta littattafai ga manoman kasar Sin. To, yanzu ga bayanin. Kwararru masu aikin likitanci na kasar Chile sun nuna cewa, game da mutanen da suka kamu da cuttuttukan jijiyoyin jini na zuciya da na kwakwalwa, kashi 90 cikin dari daga cikinsu ne ba su iya zama yadda ya kamata ba, kuma hanyar zaman rayuwa ta kiwon lafiya za ta taimaka wa yawancin mutane wajen kau da damuwarsu ta kamuwa da ciwon toshewar jijiyoyin jini na zuciya da na kwakwalwa.

A kwanan nan, wata jaridar kasar Chile ta ba da labarin cewa, ta gudanar da binciken kimiyya kan wannan matsala, an gano cewa, shan taba da karuwar yawan kitsen da ke taruwa a jijiya, wanda ke hana jini gudu su muhimman dalilai ne da suka haddasa toshewar jijiyoyin jini na zuciya da na kwakwalwa, haka kuma bacin rai zai kara hadarin kamuwa da cuttuttukan jijiyoyin jini na zuciya da na kwakwalwa. Sabo da haka, kiyaye yin zaman rayuwa ta hanyar kiwon lafiya da kuma faranta rai za su ba da taimako wajen magance irin ciwace-ciwacen.

Ban da wannan kuma kwararrun kasar Chile sun bayyana cewa, cin abinci da shan abin sha yadda ya kamata ba kawai zai ba da taimako wajen rage yawan kitsen da ke taruwa a jijiya kawai ba, a'a har ma zai iya kiyaye nauyin jiki da kuma bugun jini kamar yadda ya kamata. Kuma kwararru sun ba da shawara cewa, ya kamata a kara cin abincin da ke kunshe da cellulose, kamar 'ya'yan itatuwa da kayayyakin lambu da wake iri iri. Ban da wannan kuma ya kamata a kara cin kifi da madara da kuma man zaitun.

Bugu da kari kuma kwararru sun bayyana cewa, motsa jiki zai taka muhimmiyar rawa wajen kyautata lafiyar jijiyoyin jini na zuciya da na kwakwalwa. Suna ganin cewa, ya fi kyau baligai su rika motsa jiki har rabin awa a ko wace rana, kuma ya kamata samari su rika motsa jiki kimanin awa guda a ko wace rana.

A 'yan kwanakin nan da suka gabata, kwararru na asibitin Rascondes na birnin Santiago, babban birnin kasar Chile sun gudanar da bincike kan mutane 700 da suka kamu da cuttuttukan toshewar jijiyoyin jini na zuciya da na kwakwalwa, daga baya kuma sun gano cewa, mutane da yawansu kashi 10 bisa dari shekarunsu bai kai 40 da haihuwa ba, kuma a cikin shekara guda kafin su kamu da ciwon, sun gamu da al'amuran bakin ciki, kamar kisan aure da mutuwar iyalansu. Shi ya sa kwararru suka nuna cewa, wannan ya shaida cewa, bacin rai wani mihimmin dalili ne da ya haddasa cuttuttukan jijiyoyin jini na zuciya da na kwakwalwa. Sabo da haka kwararru sun jaddada cewa, kasancewa cikin farin ciki zai ba da taimako sosai wajen magance ciwon toshewar jijiyoyin jini na zuciya da na kwakwalwa.