Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-03-06 18:46:11    
Mutanen waje sun bayyana fahimtarsu dangane da "duniya mai jituwa" da "bunkasa cikin lumana"

cri

A cikin rahoton ayyukan gwamnati da firaministan kasar Sin, Wen Jiabao ya bayar a gun taron shekara shekara na majalisar wakilan jama'ar kasar Sin da aka bude a jiya ranar 5 ga watan Maris, Mr.Wen ya ce, Sin za ta tsaya tsayin daka a kan bin hanyar samun bunkasuwa cikin lumana, kuma tana son yi kokari ba da kasala ba tare da jama'ar kasashe daban daban don raya duniya mai jituwa da ke da dadadden zaman lafiya da albarka. Bayan haka, a gun taron manema labaru da aka shirya yau a nan birnin Beijing, ministan harkokin waje na Sin, Mr.Li Zhaoxing ya bayyana matakan da Sin za ta dauka a wajen aiwatar da akidar "duniya mai jituwa" da ta "bunkasa cikin lumana". To, amma yaya mutanen waje suke ganin wadannan akidoji biyu?

A cikin rahoton ayyukan gwamnati da ya bayar a ran 5 ga wata, firaministan kasar Sin, Wen Jiabao ya bayyana akidar "duniya mai jituwa" da ta "bunkasa cikin lumana". Ya ce,"Raya duniya mai jituwa na nufin zaman daidaici da tabbatar da dimokuradiyya a fannin siyasa da moriyar juna da hada kan juna a fannin tattalin arziki da yin musanyar al'adu da samun ci gaba tare a wannan fanni, ta hanyar aiwatar da hadin gwiwar aminci a tsakanin kasa da kasa, a fuskanci kalubale irin na gargajiya da ba na gargajiya ba da ke gaban duniya a fannin tsaro, da tabbatar da dadaddaden zaman lafiya da samun albarka tare. A halin da duniya ke ciki yanzu, ya kamata mu daga tutar zaman lafiya da ci gaba da hadin gwiwa, mu nace ga bin hanyar bunkasuwa cikin lumana."

A yayin da ministan harkokin waje na kasar Sin, Mr.Li Zhaoxing ke bayyana matakan da Sin za ta dauka a wajen aiwatar da akidar "duniya mai jituwa" da "bunkasa cikin lumana". Ya ce,"Muna dukufa kan bunkasa zaman lafiya da zaman daidaici da juna da samun moriyar juna da hadin kan juna da kuma ci gaba tare a tsakanin kasa da kasa a fannin harkokin diplomasiyya. Muna neman zama lafiya da amincewa da juna da kasashen da ke makwabtaka da mu, muna son daidaita sabanin ra'ayoyinmu ta hanyar yin shawarwari da dai sauran hanyoyin diplomasiyya, don neman tabbatar da tsaro da dadadden zaman lafiya, mu sa kaimi ga yin mu'amala da koyi da juna a tsakanin al'adu iri daban daban, mu raya zaman al'umma mai bayar da kariya ga halittu da kuma kiyaye muhalli."

Hakika, wannan ba sau na farko ba ne da shugabannin Sin suka bayyana wadannan akidoji. A cikin 'yan shekarun baya, sau tari ne shugabannin Sin suka tabo magana a kan su. A sa'i daya kuma, kasashen duniya suna ta kara sabawa da wadannan akidoji, akidojin suna kuma kara samun amincewa daga gamayyar kasa da kasa. A ganin Mr.Anil K. Gupta, wani shehun malami a jami'a Maryland ta Amurka, kirar da gwamnatin Sin ta yi dangane da "raya duniya mai jituwa" tana da nasaba da "kama hanyar bunkasa cikin lumana", ya ce,"A ganina, akidar bunkasa cikin lumana ya samu asali daya ne da akidar duniya mai jituwa. Bunkasa cikin lumana na nufin huldar jituwa da ke tsakanin Sin da sauran kasashe. Wata muhimmiyar ma'ana ta bunkasa cikin lumana shi ne samun nasara tare, a maimakon ra'ayin nan na cin moriya da bangare daya ke yi ne kawai. Bunkasuwar Sin ba ta nufin hasara ga sauran kasashe."

Bayan haka, jakadan kasar Thailand a Sin, Mr.Jullapong Nonsrichai ya nuna yabo sosai a kan bayanin da abin ya shafa da ke cikin rahoton ayyukan gwamnati da firaministan kasar Sin ya bayar, ya ce,"A cikin rahotonsa, firaministan Sin, Wen Jiabao ya yi nuni da cewa, bunkasuwar kasar Sin ta kasance cikin zaman lafiya da kwanciyar hankali, wannan shi ma abu ne da kasashe daban daban ke sa kulawa. Sabo da Sin babbar kasa ce, shi ya sa sauran kasashe suna mai da hankulansu a kan bunkasuwarta. Amma Sin ta jaddada bunkasuwarta cikin lumana, wannan ya faranta ran sauran kasashe.(Lubabatu)