Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-03-06 18:34:29    
'Yan jarida na kasashen waje suna cigaba da zura ido kan tarurrukan majalisu biyu na kasar Sin

cri

Ran 5 ga wata, bayan an soma taron shekara-shekara na majalisar wakilan jama'ar duk kasar Sin, wato hukumar koli ta kasar Sin, a nan birnin Beijing, wasu kafofin watsa labaru na kasashen waje sun sha bayar da labaru a kan tarurrukan da majalisu biyu na kasar Sin ke yi.

Ran 6 ga wata, manyan jaridun kasar Australiya sun yi rahoto kan jawabin da Mr. Wen Jiabao firaministan kasar Sin ya yi kan ayyukan gwamnatin kasar. Suna ganin cewa, jawabin da Mr. Wen Jiabao ya yi ya nuna cewa, kasar Sin za ta rika bunkasa tattalin arziki lami lafiya.

Jaridar "Nouvelles D'europe" ta birnin Paris ta yabawa rahoton da Mr. Wen Jiabao ya yi. a sa'i daya kuma, jaridun kasar Italiya kamar "La Repubblica", da "Couriere Dela Sierra" sun mai buga labaru cewa, shirin dokar ikon mallakar dukiyoyi da shirin dokar buga haraji kan kudin shiga da masana'antu ke samu sun jawo hankulan kafofin watsa labaru sosai.

Kamfanin dilancin labaru na kasar Romaniya ya ce, abin da ya cancanci a lura da shi, shi ne Mr. Wen Jiabao ya jaddada cewa, gwamnatin kasar Sin za ta yi kokari don rage banbancin da ke tsakanin birane da kauyuka a shekarar da muke ciki.

Kamfanin dilancin labaru na AP na kasar Amurka ya yi rahoton cewa, gwamnatin kasar Sin za ta kara kashe makudan kudade wajen kyautata zaman rayuwar jama'ar birane da kauyuka da sauran wurare wadanda ke fama da talauci.

Kamfanin dilancin labaru na Reuters ya bayar da labarin cewa, Mr. Wen Jiabao ya nuna cewa, kasar Sin za ta kara kokari don tsimin makamashi da rage fitar da abubuwa da ke gurbata muhalli a shekarar 2007.