Sabo da ya zuwa karshen watan jiya, kasar Iran ba ta daina tace sinadarin uranium ba bisa umurnin yarjejeniyar kwamitin sulhu na M.D.D., yaya makomar batun nukiliya na Iran yana jawo hankulan mutane sosai. A cikin 'yan kwanakin da suka wuce, kasar Iran ta dauki matakan diplomasiyya da dama, wato shugaban kasa Mahmud Ahmadinejad ya kai wa kasashen Sudan da Saudi Arabiya ziyara, mataimakin ministan harkokin waje na kasar malam Abbas Araghchi ya kuma kai ziyara ga kasashen Sin da Japan. Lokacin da kwamitin sulhu na M.D.D. yake shirin fitar da wata sabuwar yarjejeniya game da batun nukiliya na Iran, wane irin buri ne kasar Iran take son cimmawa? Ko irin wadannan matakan diplomasiyya za su yi amfani? Yanzu ga wata hirar da aka yi a tsakanin wakiliyarmu da Mr. Hua Liming, tsohon jakadan kasar Sin da ke kasar Iran.
A ganin Mr. Hua, yanzu kasar Iran tana fuskantar matsin lamba mai tsanani daga kasar Amurka. Da farko dai, yanzu, kasar Amurka tana tanadar jiragen ruwa masu daukan jiragen sama guda 2 da makamai masu linzami a shiyyar tekun Pasha da sauran karfin soja a yankunan da ke kewayan kasar Iran. Bugu da kari kuma, kasar Amurka tana shirin sake sanya takunkumi kan kasar Iran. Sabo da haka, Mr. Hua ya yi nazari cewa, lokacin da take fuskantar motsin lamba sosai da ake yi mata, kamar yadda ta taba yi a da, kasar Iran ta dauki kwararan matakai da matakai masu laushi. "Da farko dai, kasar Iran ba ta son bayyana hali maras karfi da take ciki a gaban kasar Amurka ba. Sabo da haka, a watan jiya, kasar Iran ta yi ayyukan atisaye har sau da yawa. Shugabanni da manyan jami'ai na kasar sun kuma bayar da kwararan matakansu. A waje daya kuma, kasar Iran ba ta son ganin aukuwar takunkumi ko farmaki da za a yi mata, wato tana son neman sulhu ko yin shawarwari. Tun da haka, yanzu kasar Iran tana cikin hali mai yakini wajen yin ayyukan diplomasiyya, har ma tana son halartar taro da kasar Amurka tare kan batun Iraki."
A ganin Hua Liming, ayyukan diplomasiyya da kasar Iran ta dauka sun bayyana cewa, ko da yake yanzu an ware kasar Iran sosai, amma tana yin ayyukan diplomasiyya cikin hali mai yakini. A cikin wadannan ayyukan diplomasiyya da take yi, ziyarar da ta fi muhimmanci kuma ta fi jawo hankulan mutane ita ce, ziyarar da shugaban kasar Iran ya kai wa kasar Saudi Arabiya. "Bayan da dangantakar da ke tsakanin kasashen Amurka da Iran ta shiga mawuyacin hali, muhimmin matakin diplomasiyya da kasar Amurka ta dauka shi ne neman hadin kan kasashen Larabawa. Kasashen da ke yankin Gabas ta tsakiya kasashen musulmai ne na darikar Sunni. Musamman tana fatan za ta iya hada kan kasashen Saudi Arabiya da Masar da Jordan domin yin yaki da kasar Iran. Sabo da haka, a hakika dai, ziyarar da shugaba Ahmadinejad na kasar Iran ya yi a kasar Saudi Arabiya wata gasa ce da ake yi a tsakanin Amurka da Iran. Muhimmin burin da kasar Iran take son cimmawa shi ne lalata hadin guiwar da kasar Amurka take son yi da kasashen Larabawa na darikar Sunni da ke yankin Gabas ta tsakiya."
Game da ziyarar da shugaban kasar Iran ya kai a kasar Sudan, Mr. Hua ya bayyana cewa, ko da yake kasar Sudan ma kasa ce ta musulmi, amma ita da kasar Iran suna rukuni daya, wato dukkansu suna adawa da kasar Amurka. Sabo da haka, suna kara jaddada yin hadin guiwa da daidaita matsayinsu kan wasu batutuwan kasa da kasa a tsakaninsu. Amma game da ziyarar da mataimakin ministan harkokin waje na kasar Iran ya kai wa kasar Sin da Japan, a bayyane ne yana son lallashin wadannan kasashe biyu da su taka rawarsu a zauren kwamitin sulhu na M.D.D. domin kasar Iran za ta iya kauracewa daga takunkumi ko raguwar matsin lamba da take fuskanta.
Yanzu, batun da ya fi jawo hankulan mutane shi ne, ko wadannan ayyukan diplomasiyya da kasar Iran take yi za su yi amfani? Mr. Hua Liming yana ganin cewa, za a kara dudduba su. Alal misali, dangantakar da ke tsakanin kasar Iran da kasar Saudi Arabiya wadda take da armashi tana yin tasiri ga wadannan ayyukan diplomasiyya. "A kan addinin da suke bi, kasar Iran tana bin darikar Shiite, amma kasar Saudi Arabiya tana bin darikar Sunni. Sannan kuma, kasashen Iran da Saudi Arabiya wato muhimman kasashe ne da ke fitar da man fetur dukkansu manyan kasashe ne `a yankin tekun Pasha, kuma dukkansu suna da karfi. Sabo da haka, dukkansu suna yin muhimmin tasiri ga yankin da suke ciki. Za su iya yin hadin guiwa da hada kai a fannoni daban-daban."
Bugu da kari kuma, Mr. Hua yana ganin cewa, batun nukiliya na Iran yana shafar moriyar bangarori daban-daban. Za a sha wuyar fitar da kuduri daban a zauren kwamitin sulhu na M.D.D. Kafin kwamitin sulhu na M.D.D. ya sake sa hannu kan batun, kasar Iran tana da lokacin komawa kan tebur na yin shawarwari. (Sanusi Chen)
|