Ana iya samun manoma kusan miliyan 800 a kasar Sin, shi ya sa lafiyarsu tana da matukar muhimmanci. Amma sabo da kasancewa rashin raya tattalin arziki da zamantakewar al'umma tsakanin birane da kauyuka cikin daidaici a kasar Sin, shi ya sa a kauyukan kasar Sin, musamman ma a kauyukan da ke yammacin kasar Sin, har kullum matsayin jiyya da kiwon lafiya yana baya baya, kayayyakin aikin likitanci ba su wadata ba, kuma an rasa kwararru masu aikin likitanci, ban da wannan kuma wasu manoman wurin ba su da kudin ganin likita sabo da talauci. Amma a 'yan shekarun nan da suka gabata, kasar Sin ta kara zuba kudade ga yankunan da muka ambata a baya wajen aikin jiyya da kiwon lafiya. To, a cikin shirinmu na yau, za mu shiga kauyuka na birnin Chongqing da ke kudu maso yammacin kasar Sin, mu ga sauye-sauyensu.
Unguwar Qianjiang wata unguwa ce ta birnin Chongqing, wadda yawan mutanenta ya kai dubu 500, kuma yawancinsu suna da zama a kauyuka. Wata rana, Feng Xiaomei, wata manomiya ce da ke da zama a kauyen Liming ta unguwar Qianjiang ta dauki yaronta mai shekara 1 da haihuwa zuwa asibiti don yin masa allurar rigakafin cutar hanta irin na B. Bayan da aka gama yin allurar, Madam Feng ta mika wa likita wata takarda mai launin kore a maimakon biyan kudi. Gwamnatin kasar Sin ta bayar da wadannan takardu ne domin yin allura ba tare da biyan kudi ba.
Madam Li Jie, wata likita ce da ke aikin a cikin wannan asibiti ta gaya wa wakilinmu cewa, bayan da aka fara yin wa yara allurar rigakari ba tare da biyan kudi ba, yawan yaran da suka zo aisibiti don yin allura ya samu karuwa a bayyane, Kuma ta ce, "a da, sabo da ana karbar kudi, shi ya sa iyayen yara ba su son zuwa asibiti don yin wa yaransu allurar rigakari ba. Amma yanzu ba a bukatar ko kwabo, shi ya sa kusan dukkan yara an yi musu allurar rigakafi, ta haka an ba da tabbaci ga lafiyar yara."
Samar da takardun yin allurar rigakafi wani misali ne da unguwar Qianjiang ta bayar wajen kara zuba kudade kan jiyya da kiwon lafiya. Bayan shekara ta 2003, unguwar Qianjiang ta zama daya daga cikin dungumomi da unguwoyin birnin Chongqing da aka yin gwajin tafiyar da tsarin jiyya na hadin gwiwa na kauyukan kasar Sin irin na sabon salo. A ko wace shekara, muddin ko wane manomin wurin ya biya kudi yuan 10, zai iya samun asusun jiyya na hadin gwiwa da gwamnatin kasar Sin da kuma gwamnatin wurin suke bayawa wanda yawansu ya kai yuan 50. Ban da wannan kuma, idan manoma sun je asibiti don ganin likita, to za a iya maida kudin da suka kashe da yawansu ya kai kashi 40 cikin dari. Kuma idan sun kwanta a asibiti, to za a maida kudin da suka kashe da yawansu ya kai kashi 65 cikin dari. Sabo da yanzu manoma sun kashe kudade kadan wajen ganin likita, shi ya sa suna son shiga tsarin jiyya na hadin gwiwa irin na sabon salo. Ya zuwa watan Disamba na shekarar da ta gabata, manoman da yawansu ya kai kashi 70 cikin dari na unguwar Qianjiang sun shiga tsarin.
A cikin asibitin kauyen Zhongtang na yankin Qianjiang, wakilinmu ya ga Zhu Xiaobing wanda ya koma gida ba da jimawa ba bayan da ya gama yin aiki a sauran birane. A ranar da safe, zazzabi mai zafi ya kama diyarsa. Kuma ya gaya mana cewa, a wannan karo, gaba daya ya kashe yuan 8 kawai wajen ganin likita, ciki har da yin ragista, da gwajin jini don gano cuta, da kuma sayen magunguna. Kuma ya ce, "yanzu yana da sauki gare mu wajen ganin likita, kuma likitoci sun nuna kulawa sosai ga wadanda ke fama da cuttuttuka. Ni da matata da kuma diyata dukkanmu mun shiga tsarin jiyya na hadin gwiwa na kauyuka. Lokacin da matata ta haifi diyata, an soke biyan kudi fiye da yuan dubai da muka kashe. Wannan tsarin da gwamnatin kasar Sin ta tsara ya kawo mana alheri sosai, kuma ina fatan zai iya ci gaba da amfana wa manomanmu."
A unguwar Qianjiang, ban da kara taimakon kudi ga mazaunan wurin kai tsaye, gwamnatin wurin ta zuba kudade masu yawa wajen raya muhimman kayayyakin jiyya domin kyautata ayyukan ba da hidima wajen jiyya na kiwon lafiya na kauyuka. Luo Kui, shugaban hukumar kiwon lafiya ta unguwar Qianjiang ya bayyana cewa, "a da, kwarewar aikin likitancin kauyuka babu kyau, shi ya sa fararren hulan wurin ba su iya warware matsalolin da suke fuskata wajen kiwo lafiya ba. Haka kuma ba a iya samun sauran nagartattun kayayyakin jiyya a kauyukan ba sai dai abin auna jiki da abin auna yanayin zafin jiki da kuma abin auna bugun jini."
A 'yan shekarun nan da suka gabata, gwamnatin yankin Qianjiang ta kara zuba jari wajen raya asibitocin garuruwa da na kauyuka. Ya zuwa yanzu, asibotocin kauyuka da na gundumomi da kuma cibiyoyin kiwon lafiya ta kananan unguwanni da yawansu ya kai 15 sun riga sun samun bunkasuwa sosai. Kande Gao)
|