Kabilar Lisu ta dadde tana nan kasar Sin. Yawancin 'yan kabilar suna zama a shiyyar Nujiang ta kabilar Lisu mai cin gashin kanta da wasu gundumomi na lardin Yunnan. A waje daya kuma, wasu suna zama a lardin Sichuan. Bisa kididdigar da aka yi a duk fadin kasar Sin a shekara ta 2000, yawan mutanen kabilar Lisu ya kai fiye da dubu 630. Suna amfani da yaren Lisu. Sun taba yin amfani da harufai iri 3, amma yanzu suna amfani da harufai da aka kago bisa harufan Latin.
Kafin shekarar 1949, tattalin arziki da zaman al'ummar kabilar Lisu suna samun cigaba cikin halin maras daidaito. 'Yan kabilar wadanda suke zama a shiyoyyin Lijiang da Weisi da Yongsheng da Yunlong da Lanping da Baoshan na lardin Yunnan da lardin Sichuan suna cikin zaman al'ummar mulkin kama karya, amma 'yan kabilar Lisu wadanda suke zama a yankunan tsaunin Liangshan suna cikin zaman al'ummar bauta.
Bayan da aka kafa Jamhuriyar Jama'ar Sin a watan Oktoba na shekarar 1949, gwamnatin kasar Sin ta dauki manufofi iri iri kuma ta yi gyare-gyare kan yankunan kabilar Lisu bisa halin da suke ciki ta fuskar tattalin arziki da zaman al'umma. A watan Agusta na shekarar 1954, an kafa shiyyar Nujiang ta kabilar Lisu mai cin gashin kanta ta lardin Yunnan. Yau fiye da shekaru 50 da suka wuce, 'yan kabilar Lisu sun sari gonaki da gina ayyukan ban ruwa da raya masana'antu iri iri tare da kuma shimfida layin samar da wutar lantarki da gidajen waya a yankuna daban-daban na kabilar. Haka kuma an samu cigaban aikin ilmi da na kiwon lafiya. Yanzu 'yan kabilar Lisu suna da daliban jami'a da malamai da likitoci da masanan ilmin kimiyya nasu.
'Yan kabilar Lisu sun kware kan wakoki da raye-raye. Lokacin da ake shirya bikin aure da gina gidaje tare da kuma bikin murnar girbi, tabbas ne su waka da rawa kamar yadda suke so.
Ko da ya ke 'yan kabilar Lisu suna zama a wurare daban-daban, amma suna sanye da tufafi kusan iri daya. Maza sun fi son sanye da gajeriyar riga da wando. Tsawon wando da suke sanye ya kai guiwa kawai. Wasu kuma suna nada rawani da zanen baki. Maza sun fi son rataya wata wuka a kan kugu na hagu tare da wata jakar kibiya a kan kugu na dama. Mata suna sanye da gajeriyar riga tare da wani tsawon buje. Tufafin da matan kabilar Lisu suke sanye suna da launi iri iri.
'Yan kabilar Lisu suna cin masara da nama. Maza ko mata dukkansu sun iya shan giya.
'Yan kabilar Lisu suna da ladabi sosai, musamman sun fi girmama dattawa.
Bisa al'adar kabilar Lisu, wani saurayi yana iya auren mace daya. Matasa suna da 'yancin neman abokan soyayya, amma iyaye ne suke tabbatar da aurensu.
A da, 'yan kabilar Lisu sun bin addinan gargajiya na kasar Sin, amma tun daga farkon karni na 20 da ya wuce, bayan da isowar addinin Kirista a yankunansu, wasu sun fara bin addinin Kirista da Katolika.
|