Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-03-05 18:17:02    
Mr Wen Jiabao, firayim ministan kasar Sin ya gabatar da rahoto kan ayyukan gwamnati

cri

Ran 5 ga wata da safe, a nan birnin Beijing, an bude taron shekarar nan na majalisar wakilan jama'ar kasar Sin wadda ita ce hukumar koli ta kasar Sin. Inda a madadin gwamnatin kasar, firayim minista Wen Jiabao ya gabatar da rahoto kan ayyukan gwamnati ga kimanin wakilai 3,000 da ke halartar taron nan. Wasu manyan manufofi da ya gabatar a cikin rahotonsa, ba ma kawai sun gaji tsoffin manufofin gwamnatin kasar ba, har ma sun nuna hanyoyi da za a bi wajen magance matsaloli da ake fuskanta a yanzu. Manyan ayyuka da gwamnatin kasar ke yi a shekarar nan su ne, kawo fa'ida ga jama'a da arzutar da manoma. Gwamnatin kasar za ta yi kokari wajen kawar da wahalhalu da jama'a ke sha don kara kafa zamantakewar al'umma mai jituwa. Yanzu za mu bayyana muku wasu manyan abubuwa da ke cikin rahoton nan.

Rahoton mai kalmomi 20,000 ya kasu cikin kashi 6. Ban da ayyukan shekarar bara da ya waiwaya, da manyan shirye-shiryen ayyuka da za a yi a shekarar nan, sauran kashi-kashi hudu su ne, gaggauta bunkasa tattalin arziki da kyau kuma cikin sauri, da sa kaimi ga kafa zamantakewar al'umma mai jituwa, da zurfafa aikin gyare-gyare da kara bude wa kasashen waje kofa, da kuma inganta gyare-gyaren gwamnati da aikin gina shi.

A cikin sabuwar shekara, ba ma kawai kasar Sin za ta ci gaba da taka tsantsan wajen aiwatar da harkokin kudin gwamnatin da na kudi mai inganci ba, har ma za ta kara aiwatar da sabbin manufofi game da zuba kudi wajen yin manyan ayyuka a kauyuka da sauransu. Firayim minista Wen Jiabao ya bayyana wa wakilai mahalartan taron sakamako da aka samu wajen daidaita matsalolin jinkirtar da biya wa ma'aikata 'yan ci-rani albashinsu da aka fara yi a fannin gine-gine a shekarar 2004. Ya yi farin ciki da cewa, "yanzu, an kusa kammala wannan aiki, yawan albashin da aka biya wa ma'aikata 'yan ci-rani ya kai kudin Sin Renminbi Yuan biliyan 33. An kiyaye halalen iko da moriyar ma'aikata 'yan ci-rani ta hanyar tsaida manufofi game da daidaita matsalolin ma'aikata 'yan ci-rani da kuma aiwatar da su."

A karo na farko ne kasar Sin ta gabatar da manufar bunkasuwar tattalin arzikinta tare da wasu manyan sharuda. Da firayim minista Wen Jiabao ya tabo magana a kan wannan, sai ya bayyana cewa, "bayan da aka yi la'akari da bukatu da sauran abubuwa da yawa, mun gabatar da manufa cewa, jimlar kudi da kasar Sin za ta samu daga wajen samar da kayayyaki a gida wato GDP zai karu da wajen kashi 8 cikin dari a shekarar nan. Kamata ya yi, a yi ayyuka musamman domin kyautata tsari, da inganta aikin samar da kayayyaki, da tsimin makamashi da danyun kayayyaki da ake amfani da su da kuma rage fitar da abubuwa da ke gurbata muhalli, ta yadda za a bunkasa harkokin tattalin arziki da kyau kuma cikin sauri. "

Ka zalika gwamnatin kasar Sin tana mai da hankali sosai ga matsalar babban gibi da ke kasancewa a tsakanin mazaunan birane da na kauyuka a fannin zaman rayuwa. A cikin sabuwar shekara, gwamnatin kasar Sin za ta kara kashe kudin Sin Yuan biliyan 52 daidai da misalin dalar Amurka biliyan 6.5 don ba da taimako ga aikin noma da kauyuka da kuma manoma. Mr Wen Jiabao ya kara da cewa, "ya kamata, a bana, a kafa tsarin ba da tabbaci ga zaman rayuwar mazaunan kauyukan kasar baki daya bisa matsayi mafi kankanta. Wannan wani babban mataki ne da aka dauka don kafa zamantakewar al'aumma mai jituwa. Kafa irin wannan tsari yana da muhimmanci sosai ga tabbatar da zaman daidaici a tsakanin jama da kafa zamantakewar al'umma mai jituwa." (Halilu)