Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-03-05 13:59:09    
Kasar Sin ta kusan daidaita batun bin albashin da ba a biya wa manoma 'yan cirani ba gaba daya

cri
A shekarar 2004, gwamnatin kasar Sin ta bayar da shirin cewa, za ta daidaita batun bin albashin da ba a biya wa manoma 'yan cirani ba da batun bin kudaden ayyukan da ya kamata a biya a cikin shekaru 3. Yanzu, an riga an kusan cimma wannan burin.

Mr. Wen Jiabao ya fayyace haka ne a gun bikin kaddamar da taron shekara-shekara na majalisar dokokin kasar Sin da aka soma yi a ran 5 ga wata lokacin da yake bayar da wani rahoto kan aikin gwamnati. Ya bayyana cewa, yawan kudaden ayyukan da aka riga aka biya ya kai kashi 98.6 cikin kashi dari yayin da yawan albashin da aka biya manoma 'yan cirani ya kai kudin Renminbi yuan biliyan 33, wato kimanin dalar Amurka biliyan 4.1.

A waje daya kuma, Mr. Wen ya dauki alkawarin cewa, gwamnatin kasar Sin za ta kara saurin kafa tsarin tabbatar da ingancin rayuwa da ke dacewa da halin da manoma 'yan cirani suke ciki, musamman kafa inshora da samar da ayyukan jiyya ga manoma 'yan cirani idan sun ji rauni lokacin da suke aiki ko suka kamu da ciwo mai tsanani. (Sanusi Chen)