Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-03-05 09:17:04    
Jaridar People's Daily ta taya murnar kaddamar da taron shekara-shekara na NPC

cri
A kan jaridar "People's Daily" ta kasar Sin da aka wallafa ta a ran 5 ga wata, an buga wani bayanin sharhi mai take "Neman cigaba a kan hanyar kimiyya" domin murnar cikakken zama na 5 na majalisar dokokin kasar Sin na 10.

Wannan sharhi ya bayyana cewa, cikakken zama na 5 na majalisar dokokin kasar Sin wani muhimmin al'amarin siyasa ne a nan kasar Sin. Wannan taro yana da muhimmanci sosai kan yadda za a sa kaimi ga dukkan 'yan jam'iyyar kwaminis ta kasar da jama'ar duk kasar da su yi aikin yin gyare-gyare da neman bunkasuwa da tabbatar da kwanciyar hanjkali yadda ya kamata da ciyar da aikin raya wata zaman al'ummar gurguzu mai matsakaicin karfi kuma mai jituwa.

Wannan sharhi ya kuma jaddada cewa, tsara shirye-shiryen "Dokar Ikon Mallakar Dukiyoyi" da "Dokar Buga Haraji kan Masana'antu", ba ma kawai wani muhimmin nauyin da ke bisa wuyanmu ba wajen kafa cikakken tsarin shari'a na gurguzu da ke dacewa da halin musamman da kasar Sin ke ciki, har ma wajibabbiyar bukata ce domin raya tattalin arziki da zaman al'ummar kasar Sin. (Sanusi Chen)