Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-03-04 18:22:00    
Tsarin majalisar wakilan jama'a babban tsarin siyasa ne da jama'ar Sin ke tafiyar da harkokin mulki

cri
A gobe Litinin, za a yi taron shekara shekara na majalisar wakilan jama'ar kasar Sin, wato NPC, wadda kuma ta kasance hukumar koli da ke gudanar da harkokin mulkin kasar Sin. Taron dai wani muhimmin al'amari ne na harkokin siyasa na jama'ar kasar Sin, wanda zai tsai da burin da Sin za ta cimma cikin sabuwar shekara a fannin bunkasuwa, kuma zai yi bincike a kan daftarin dokokin da ke shafar zaman rayuwar jama'a da kuma kada kuri'a a kansu. To, yanzu bari mu yi muku bayani a kan tsarin majalisar wakilan jama'ar kasar Sin.

Bisa tsarin mulkin kasar Sin, mulkin kasa yana hannun jama'arta, kuma hukumar da jama'a ke amfani da ita wajen gudanar da harkokin mulkin kasa ita ce majalisar wakilan jama'ar duk kasa da kuma majalisun wakilan jama'a na wurare daban daban. A lokacin da ake yin taron NPC, wakilan jama'a kusan 3000 wadanda suka fito daga wurare da sana'o'i daban daban na kasar Sin za su hadu a nan birnin Beijing, don tafiyar da harkokin mulkin kasa a madadin jama'ar kasar Sin biliyan 1 da miliyan 300.

Madam Wu Ailing, wata likita ce da ta zo daga lardin Sichuan da ke kudu maso yammacin kasar Sin. Ita 'yar kwamitin juyin juya hali na jam'iyyar Kuomintang ta kasar Sin ce, a yayin da ta kuma kasance daya daga cikin wakilan jama'ar kasar Sin. A matsayinta na likita da wakiliyar jama'a, tun daga shekarar 2003, sai ta gabatar da shawarar rigakafin ciwon tsagiya ga majalisar NPC, kuma mataimakiyar firaministan Sin, Madam Wu Yi ita ce ta kula da tabbatar da wannan shawarar da ta gabatar. Madam Wu Ailing ta ce,"A cikin 'yan shekarun baya, cutar tsagiya ta sake bullowa a wasu wurare na kasar Sin, bayan da na zama wakiliyar jama'a, sai na gabatar da wannan shawarar. Sakamakon kirar da na yi tare da sauran wakilai, an maido da kungiyar kula da harkokin rigakafin cutar tsagiya a kasar Sin, kuma mataimakiyar firaministan kasar Sin, Madam Wu Yi ita da kanta ce take shugabantar kungiyar. Gwamnati ta nuna gatanci ga wuraren da ke fama da yaduwar cutar tsagiya a fannonin manufa da kudi da dai sauransu. Sakamakon matakan da aka dauka yadda ya kamata, an shawo kan yaduwar cutar tsagiya."

Madam Wu Ailing daya ce kawai daga cikin wakilan jama'ar duk kasa kusan 3000, kuma shawarar da ta gabatar ita ma daya ce daga cikin shawarwari dubai da majalisar wakilan jama'ar kasar Sin ta samu a ko wace shekara. Ban da wakilan jama'a na duk kasa, akwai kuma wakilan jama'a na matakai daban daban da yawansu ya wuce miliyan 2 da dubu 800. To, amma ta yaya ake fitar da wadannan wakilan jama'a? A bayane ne tsarin mulkin kasar Sin ya tsara cewa, an zabi wakilan jama'a na matakai daban daban ne ta hanyar dimokuradiyya. Wa'adin aiki na ko wane wakilin jama'a ya kai shekaru biyar, kuma da wa'adin aikinsu ya cika, za a sake gudanar da zaben wakilan jama'a. A kasar Sin, dukan jama'ar kasar da shekarunsu suka kai 18 da haihuwa, suna da ikon zaben wakilan jama'a ko kuma shiga takarar neman zama wakilan jama'a.

Daidai sabo da an zabi wakilan jama'a ta hanyar dimokuradiyya, kuma suna wakiltar moriyar jama'a, shi ya sa jama'a suna iya sanar da sassan da abin ya shafa matsalolin da suka gamu a aikinsu ko zaman rayuwarsu ta bakin wakilansu na matakai daban daban. Matsalolin wasunsu sun fitar da dokoki, wasu kuma gwamnati ta dauki matakai wajen daidaita su. A yayin da yake yin bayani a kan tsarin nan na majalisar wakilan jama'a, Mr.Wu Bangguo, shugaban zaunannen kwamitin majalisar wakilan jama'ar kasar Sin, ya ce,"Sin tana gudanar da tsarin majalisar wakilan jama'ar kasar Sin a matsayin tsarinta na siyasa. Ta wannan tsari ne jama'a suke rike da makomar kasa da ta al'umma a hannunsu. Wakilan jama'a na matakai daban daban, sun zo ne daga bangarori daban daban, suna wakiltar jama'a na bangarori daban daban, a madadin jama'a ne suke tsai da kuduri a kan manyan batutuwan kasa da na wurare daban daban."

Mr.Zhang Chunsheng, wani masanin ilmin dokoki, ya bayyana aihinin tsarin majalisar wakilan jama'a cewa," yanzu akwai mutane biliyan 1 da miliyan 300 a kasar Sin, a yayin da suke tafiyar da harkokin mulki na kasar, dole ne su sami wani tsarin da ya dace wanda kuma ake iya amfani da shi. Tsarin majalisar wakilan jama'a ba ma kawai majalisar wakilan jama'a ba, har ma cikakken tsari ne na harkokin mulkin kasar Sin wanda ke da majalisar wakilan jama'a a matsayin cibiyarta."(Lubabatu)