Ran 4 ga wata, a nan Beijing, kakakin taron shekara-shekara na majalisar wakilan jama'ar kasar Sin Mr. Jiang Enzhu ya bayyana cewa, kasar Sin tana aiwatar da dokoki iri-iri wajen 230 a shekarar 2007 da muke ciki, a galibi dai za ta samar da tsarin dokoki na gurguzu mai sigogin musamman na kasar Sin.
Mr. Jiang ya kara da cewa, a shekarar bana, a lokacin da yake ci gaba da kara karfin kafa dokoki kan harkokin tattalin arziki, a sa'i daya kuma, zaunannen kwamitin majalisar wakilan jama'ar kasar Sin zai dora muhimmanci kan kara karfin kafa dokoki a fannin zaman al'ummar kasa, ban da ci gaba da yin bincike kan shirye-shirye 7 kan dokar yaki da babakere da ta harkokin yarjejeniyoyin aiki, kasar Sin ta kuma yi shirin yin bincike kan shirye-shiryen dokoki 13 kan ba da inshorar zaman al'ummar kasa da dokar gudanar da harkokin mulki da karfi da dai sauransu.(Tasallah)
|