Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-03-03 18:52:16    
An bude taron CPPCC a birnin Beijing

cri
Yau a nan birnin Beijing, an bude taron shekara shekara na majalisar ba da shawara kan harkokin siyasa ta kasar Sin, wato CPPCC. Shugaban majalisar, Mr.Jia Qinglin ya bayyana cewa, majalisar CPPCC za ta ci gaba da daukar nauyin da ke bisa wuyanta na ba da shawarwari a kan harkokin siyasa da sa ido a kan harkokin siyasa ta hanyar dimokuradiyya da kuma sa hannu cikin harkokin siyasa, don ta ba da sabuwar gudummowa yadda ya kamata a wajen raya zaman al'umma mai albarka da bunkasa harkokin gurguzu na kasar Sin.

Yau Asabar da yamma, mambobin CPPCC, wato majalisar ba da shawara kan harkokin siyasa ta kasar Sin, sun hadu a babban dakin taron jama'a da ke nan birnin Beijing, don halartar taro a karo na 5 na majalisar CPPCC ta 10, wanda kuma ya kasance taro na karshe na majalisar nan ta 10. Da daidai karfe 3 ne a yamma, an bude taron.

A gun bikin bude taron, shugaban majalisar CPPCC, Mr.Jia Qinglin ya gabatar da rahoton aiki ga taron. Da farko dai, ya waiwayi nasarorin da majalisar CPPCC ta samu a shekarar da ta gabata, ya ce,"Shekara ta 2006 shekara ce da muka samu dimbin nasarori a wajen harkokin gyare-gyare da bude kofa ga kasashen waje da kuma raya harkokin gurguzu na zamani, haka kuma ta kasance shekarar da aka samu kyakkyawar bunkasuwar harkokin majalisar CPPCC. Majalisar CPPCC da kuma zaunannen kwamitinta sun dauki nauyin da ke bisa wuyansu kamar yadda ya kamata, kuma sun yi kokarin sa kaimi ga gyare-gyaren aikinsu, sun yi kokarin gudanar da nazari, sun yi kokarin raya kansu, sun sami sabon ci gaba a wajen ayyuka daban daban."

Majalisar CPPCC hukuma ce ta koli ga jam'iyyu da kabilu da bangarori daban daban a wajen yin shawarwarin siyasa, mambobin majalisar su kan gabatar da ra'ayoyinsu ko shawarwarinsu dangane da manyan manufofin kasa da kuma batutuwan da ke daukar hankulan al'umma, kuma hukumomin gwamnati su kan dauki yawancin shawarwarin a wajen tsara manufofi. An ce, tun bayan shekarar da ta gabata, gaba daya akwai shawarwari 4999 da majalisar ta gudanar da bincike a kansu da kuma mika su a hannun hukumomin gwamnati da abin ya shafa don a kula da su. Ta hanyar yin nazari a kansu da daukarsu ne, wadannan shawarwari sun taka muhimmiyar rawa a wajen sa kaimi ga bunkasuwar tattalin arziki da zama al'umma cikin daidaici da taimaka wa gwamnati wajen yanke shawara da kuma sassauta sabani iri iri a tsakanin al'umma. Bayan haka, CPPCC ta kuma kira taron zaunannen kwamitinta, don gabatar da shawarwari da ra'ayoyi kan batun kara karfin raya zaman al'umma mai jituwa irin na gurguzu, da kuma gudanar da bincike kan manyan batutuwa da kuma kara sa kaimi ga jam'iyyu daban daban da mutanen da ba su zo daga ko wace jam'iyyar siyasa ba da su ba da gudummowarsu yadda ya kamata, ta kuma yi kokarin hada kanta da jama'ar Hongkong da Macao da Taiwan da Sinawa mazaunan kasashen waje da kuma sada zumunci a tsakaninsu, ta yi kokarin bunkasa harkokin diplomasiyya da kasashen waje.

Yayin da yake tsinkayar aikin da CPPCC za ta gudanar a wannan shekara, Mr.Jia Qinglin ya ce,"A cikin sabuwar shekara, za mu tsaya tsayin daka a kan tsarin hadin gwiwar jam'iyyu da dama da ba da shawarwarin siyasa wanda ke karkashin jagorancin jam'iyyar kwaminis ta Sin da kuma kara kyautata shi, za mu kara bunkasa rukunin masu kishin kasa, mu nace ga bin manyan jigogi biyu na hadin kan al'umma da dimokuradiyya, mu yi kokarin daukar nauyinmu na yin shawarwari kan harkokin siyasa da sa ido a kan harkokin siyasa ta hanyar dimokuradiyya da kuma sa hannu cikin harkokin siyasa, mu gudanar da ayyuka daban daban yadda ya kamata a shekarar karshe da ke cikin wa'adin aiki na majalisar CPPCC ta wannan karo."(Lubabatu)