Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-03-03 18:00:11    
Dukkan NPC sun iso birnin Beijing

cri

Da karfe 7 da minti 20 na ran 3 ga wata da safe, kungiyar wakilan jihar Mongoliya ta gida mai cin gashin kanta ta iso birnin Beijing. Sabo da haka, dukkan wakilan majalisar dokokin kasar Sin wadanda za su halarci cikakken zama na biyar na majalisar ta 10 sun iso birnin Beijing.

A ran 5 ga watan Maris ne za a soma cikakken zama na biyar, wato taron shekara-shekara na majalisar dokokin kasar Sin a birnin Beijing. An bayyana cewa, An riga an kusan kammala dukkan ayyukan share fagen wannan taron shekara-shekara na majalisar dokokin kasar Sin, wato NPC.

Ma'aikatan da za su juya rahotannin aiki da za a gabatar a gun taron zuwa harsunan kananan kabilun kasar Sin, ciki har da harsunan Tibet da Mongoliya da Uygur da Khazak da Koriya da Yi da na Zhuang daga harshen Sinanci sun riga sun shiga mukaminsu. Bugu da kari kuma, za a juya wasu takardun taron zuwa harsunan waje. Sakamakon haka, manema labaru na kasashen waje za su iya karantu su cikin sauki. (Sanusi Chen)