Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-03-03 16:33:56    
An soma taron shekara-shekara na CCPCC a birnin Beijing

cri

Da karfe 3 na ran 3 ga watan Maris da yamma, an soma cikakken zama na biyar, wato taron shekara-shekara na majalisar ba da shawara kan harkokin siyasa ta kasar Sin, wato CCPCC a nan birnin Beijing.

A cikin rahoton aikin da Jia Qinglin, shugaban CCPCC ya bayar, an nuna cewa, a cikin shekarar 2006, majalisar CCPCC ta aiwatar da nauyin yin tattaunawa kan harkokin siyasa da dudduba ayyukan gwammati ta hanyar dimokuradiyya da halarci da dudduba ayyukan gwamnati da ke bisa wuyanta. Sannan kuma, majalisar ba da shawara kan harkokin siyasa ta kasar Sin ta kara mai da hankali kan yin nazarin tunani domin kokarin raya ta da kanta. Sabo da haka, majalisar ba da shawara kan harkokin siyasa ta kasar Sin ta samu sabon cigaba a fannoni iri iri.

Bugu da kari kuma, Jia Qinglin ya bayyana cewa, majalisar ba da shawara kan harkokin siyasa ta kasar Sin za ta ci gaba da tsayawa da kuma kyautata tsarin hada kan jam'iyyun siyasa da ba da shawarwari kan harkokin siyasa a karkashin jagorancin jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin. Kuma za ta tsaya kan matsayin bin hanyar siyasa ta gurguzu da ke dacewa da halin musamman da kasar Sin ke ciki. A sa'i daya kuma, za ta kara taka rawarta kan raya siyasar dimokuradiyya da wayin kai na gurguzu. A waje daya kuma, majalisar ba da shawara kan harkokin siyasa ta kasar za ta mai da kokarin neman cigaban tattalin arziki da zaman al'umma ta hanyar kimiyya domin neman wani kyawawan cigabansu cikin sauri a kan matsayi mafi muhimmanci lokacin da take aiwatar da nauyin da ke bisa wuyanta. (Sanusi Chen)