Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-03-03 15:05:15    
An soma taron shekara-shekara na CCPCC

cri

Da karfe 3 na ran 3 ga watan Maris da yamma, an soma cikakken zama na biyar, ato taron shekara-shekara na majalisar ba da shawara kan harkokin siyasa ta kasar Sin,wato CCPCC a nan birnin Beijing.

Muhimman ajandar da ake yi yau shi ne. 'yan majalisar fiye da dubu 2 na jam'iyyun siyasa iri iri da bangarori daban-daban sun saurari rahoton aiki da Jia Qinglin, shugaban CCPCC ya bayar a madadin zaunannen kwamitin majalisar.

Muhimman shugabannin kasar Sin ciki har da shugaban kasar Sin Hu Jintao da shugaban majalisar dokokin kasar Sin Wu Bangguo da firayin minisatan kasar Sin Wen Jiabao sun halarci bikin kaddamar da taron.

Bisa ajandar da aka tsara, za a yi kwanaki 12 ana yin wannan taron shekara-shekara na CCPCC. A gun taron, 'yan majalisar za su tattauna tare da kuma ba da shawarwarinsu kan manyan manufofin yin gyare-gyare da neman cigaban kasar Sin da batutuwan da ke shafar zaman rayuwar jama'ar kasar. (Sanusi Chen)