Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-03-02 18:39:09    
Majalisar CPPCC ta kasar Sin tana taka muhimmiyar rawa a harkokin siyasa na Sin

cri
A gobe Asabar, wato ranar 3 ga wata, za a soma taron shekara shekara na majalisar CPPCC a nan birnin Beijing, wato majalisar ba da shawara kan harkokin siyasa ta kasar Sin, kuma a lokacin, wakilan majalisar wadanda suka fito daga jam'iyyu da kabilu da kuma bangarori daban daban za su hadu a nan birnin Beijing, don tattauna harkokin kasar Sin. A matsayinta na wata muhimmiyar hukuma ta hadin kan jam'iyyu da dama da yin shawarwarin siyasa, majalisar CPPCC tana taka muhimmiyar rawa a harkokin siyasa na kasar Sin.

Madam Zhou Yuanmei wadda ke da shekaru 70 da haihuwa wakiliya ce a majalisar CPPCC har karo hudu a jere, kuma wannan shekara ta kasance ta 20 a gare ta a wajen halartar taron majalisar CPPCC. Ta gaya wa wakilinmu cewa, a gun taron majalisar CPPCC da za a yi a wannan shekara, za ta fi mai da hankalinta a kan wasu batutuwa, ta ce,"Ina aiki ne a bangaren kimiyya da fasaha, kuma abin da mu 'yan bangaren kimiyya da fasaha muke fi kulawa da shi shi ne kirkire-kirkire bisa karfin kanmu. Bayan haka, game da batun ma'aunin zaman rayuwa mafi kankanta da gyare-gyaren aikin kiwon lafiya a kauyuka, ni ma ina da wasu ra'ayoyi."

Gobe Madam Zhou da dai sauran wakilan majalisar sama da 2200 za su halarci cikakken taro a karo na 5 na kwamiti na 10 na CPPCC a babban dakin taron jama'a da ke nan birnin Beijing. An ce, a gun taron, za a fi mai da hankali a kan harkokin raya aikin noma na zamani da magance hadarurrukan kudi da gyara da kuma kulawa da kasuwannin hada-hadar cinikin gidaje da nuna adalci a tsakanin al'umma da hukunta masu cin hanci da raya al'adun al'umma da dai sauransu. Batutuwan da wakilan majalisar CPPCC za su tattauna su kan kasance abubuwan da suke fi daukar hankulan al'ummar kasar Sin a halin yanzu.

A matsayinta na wani muhimmin tsari na tattauna harkokin siyasa da hadin kan jam'iyyun dimokuradiyya daban daban da wadanda ba su zo daga ko wace jam'iyya ba da kungiyoyin jama'a da kabilu da bangarori daban daban, majalisar ba da shawara kan harkokin siyasa ta kasar Sin, wato CPPCC, hukuma ce ta koli ta yin shawarwari. Wakilan da suka fito daga jam'iyyu da kabilu daban daban wadanda ke bin addinai daban daban sun hadu don tattauna harkokin siyasa, suna iya fada albarkacin bakinsu, an kiyaye hakkinsu na dimokuradiyya yadda ya kamata. Bisa shekaru 20 da ta shafe tana kan kujerar wakiliyar majalisar, Madam Zhou ta bayyana fahimtarta dangane da majalisar nan ta ba da shawara kan harkokin siyasa ta kasar Sin. Ta ce,"Tsarin siyasa na kasar Sin ya sha bamban da irin na kasashen yammaci, tsarinmu tsari ne na hadin kan jam'iyyu da dama da yin shawarwarin siyasa, wanda kuma tsarin jam'iyyu ne na gurguzu da ke da tsarin musamman na kasar Sin. Wani babban nauyin da ke bisa wuyan majalisar CPPCC shi ne yin shawarwarin siyasa da sa ido kan harkokin kasa ta hanyar dimokuradiyya da sa hannu cikin harkokin siyasa. Wadannan ayyuka uku muhimman hanyoyi ne da jam'iyyu da kungiyoyi da kabilu da bangarori daban daban ke bi wajen shiga harkokin siyasa da ba da gudummowarsu bisa tsarin siyasa na kasar Sin.

Gabatar da shawarwari ga taron majalisar CPPCC muhimmiyar hanya ce ga wakilan majalisar da kuma jam'iyyu da kungiyoyi da suke wakilta wajen daukar nauyinsu. An ce, tun bayan taron shekara shekara na CPPCC da aka yi a shekarar bara, gaba daya akwai shawarwari 4999 da majalisar ta gudanar da bincike a kansu da kuma mika su a hannun hukumomin da abin ya shafa don a kula da su. Ta hanyar yin nazari a kansu da daukarsu ne, wadannan shawarwari sun taka muhimmiyar rawa a wajen sa kaimi ga bunkasuwar tattalin arziki da zama al'umma cikin daidaici da taimaka wa gwamnati wajen yanke shawara da kuma sassauta sabani iri iri a tsakanin al'umma.

Mr.Zhang Feng, wani shehun malami ne a hukumar nazarin CPPCC ta kasar Sin, ya ce,"CPPCC muhimmiyar hanya ce ta yin shawarwarin dimukuradiyya irin na gurguzu, kuma za ta taimaka wajen raya dimokuradiyyar gurguzu da kuma bunkasa harkokin siyasa na gurguzu, haka kuma tana da amfani wajen bayyana bukatun bangarori daban daban a fannin moriyarsu da kuma siyasa, ta yadda za a sa kaimi ga samun jituwar al'umma."(Lubabatu)