Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-03-02 18:36:34    
An kammala dukkan ayyukan share fagen cikakken zama na 5 na CCPCC

cri

A ran 2 ga wata, Mr. Wu Jianmin, kakakin cikakken zama na 5 na CCPCC, wato majalisar ba da shawara kan harkokin siyasa ta kasar Sin ta 10 ya sanar a birnin Beijing cewa, an riga an kammala dukkan ayyukan share fagen wannan taron shekara-shekara na CCPCC. Za a soma wannan taro a ran 3 ga wata bisa shirin da aka tsara.

A waje daya, Mr. Wu ya ce, muhimman ayyukan da za a yi a gun wannan taro su ne, za a saurari da dudduba rahoton aiki da zaunannen kwamitin majalisar ba da shawara kan harkokin siyasa ta kasar Sin zai gabatar da rahoton yadda ake daidaita shawarwarin da 'yan majalisar suka gabatar a cikin shekara 1 da ta gabata bayan da aka kawo karshen cikakken zama na 4 na majalisar ba da shawara kan harkokin siyasa ta kasar a shekarar bara. Sannan kuma 'yan majalisar za su halarci cikakken zama na 5 na majalisar dokokin kasar Sin na 10 tare da kuma saurara da dudduba rahoton aikin gwamnati da shirin Dokar Ikon Mallakar Dukiyoyi da shirin Dokar Buga haraji kan masana'antu da rahotonnin aiki game da kotun koli ta jama'a da hukumar bincike ta koli ta jama'a na kasar Sin da dai sauransu.

Gobe da yamma, gidan rediyon kasar Sin da gidan rediyon jama'ar kasar Sin da gidan talibijin na tsakiya na kasar Sin za su yada labarun bikin soma cikakken zama na 5 na majalisar ba da shawara kan harkokin siyasa ta kasar Sin kai tsaye cikin harsunan Turanci da Sinanci. (Sanusi Chen)