Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-03-02 17:39:18    
Gasar cin kofin duniya ta wasan softball ta mata ta jarraba aikin share fage ga taron wasannin Olympic na Beijing

cri

A matsayin wata gasar jarrabawa ta farko ta taron wasannin motsa jiki na Olympic da aka gudanar a nan Beijing, aka kammala gasar cin kofin duniya ta wasan kwallo mai laushi wato softball ta mata a kwanakin baya ba da dadewa ba a nan birnin Beijing. An gudanar da wannan gagarumar gasa ne tun daga ran 27 ga watan jiya daidai bisa abubuwan da aka tanada game da harkokin gasanni na taron wasannin Olympic na Beijing.

A matsayin wata gasar jarrabawa ta farko ta taron wasannin motsa jiki na Olympic da aka gudanar da ita a nan Beijing, irin salo mai amfani da aka bi wajen gudanar da harkokin gasar cin kofin duniya ta wasan softball ya cancanci abun koyi wajen shirya gasanni a filaye da dakunan wasan motsa jiki cikin lokaci daya yayin da ake gudanar da taron wasannin Olympic na Beijing. Ana kiran irin wannan salon tafiyar da harkokin gasanni a kan cewa ' kungiyoyi da rukunoni na filaye da dakunan wasannin Olympic'. ' Yan wadannan kungiyoyi da na rukunoni dukansu sun zo ne daga kwamitin shirya taron wasannin Olympic na Beijing. An kuma kafa sassan aiki guda 24, wadanda za su kula da harkokin gasanni, da ayyukan gini na filaye da dakunan wasa, da zirga-zirga, da tsaro da kuma ayyukan kafofin watsa labarai da dai sauransu, ta yadda za a bada tabbaci ga gudanar da taron wasannin Olympic na Beijing lami-lafiya.

Mr. Yang Shuan, mataimakin shugaban zartaswa na kwamitin shirya taron wasannin Olympic na Beijing ya bayyana, cewa gasar cin kofin duniya ta wasan kwallo mai laushi wato softball da aka yi a wannan gami, daya ce kawai dake cikin gasannin jerin jarrabawa kafin a kira taron wasannin Olympic na Beijing. A shekara mai zuwa, za a shirya gasanni makamantanta mafi yawa a fannin wasa daya-daya domin sa ido da kuma dudduba tsararrun fasahohi da harkokin shirye-shiryen gasanni daga dukkan fannoni a duk tsawon lokacin taron wasannin Olympic na Beijing a shekarar 2008.

Mr. Yang Shuan ya kara da, cewa a matsayin wani kasaitaccren taron wasannin motsa jiki, lallai ayyukan shirye-shiryen taron wasannin Olympic wani tsarin ayyuka ne mai sarkakiya.

Aikin tsaro yana da muhimmancin gaske ga kowace irin gagarumar gasa. Aikin tsaro na gasar cin kofin duniya ta wasan softball da aka yi a wannan gami yana da halayen musamman guda biyu wato na nuna halin mutumtaka da fasahohin zamani.

Kungiyoyi 16 sun halarci wannan gasa ta wasan softball. Maganar cin abinci da yin kwana na 'yan wasa da malaman koyarwa da kuma mahukunta da yawansu ya wuce 500, wata muhimmiyar magana ce. Da yake lokutan shiga gasa na dukkan kungiyoyin daban daban ne, shi ya sa otel-otel da 'yan wasa ke zama sun samar da abinci mai dadi cikin lokaci-lokaci.

Jama'a masu sauraro, kuna sane da cewa, alamun nuna manufar hanyoyin mota dake kusa da filin gasa suna da muhimmanci sosai ga aikin gudanar da wata gagarumar gasa. An kafa alamun nuna manufar hanyoyin mota da yawa a kan hanyar zuwa filin gasa ta wasan softball kuma direbobin motocin musamman na gasar din sun gane su sosai, amma duk da haka, ' yan kallo da yawa sun yi koke-koken cewa ba su samu saukin ganewa ba, kuma ba su samu saukin daukar mota domin koma gida ba bayan an gama gasa da aka yi a dare.

Game da wannan magana dai, Mr. yang Shuan ya tabbatar da, cewa ko shakka babu za a kara kyautata halin zirga-zirga a nan Beijing lokacin da ake gudanar da taron wasannin Olympic na Beijing a shekarar 2008 domin an kadddamar da wani shirin muhimman tsare-tsare na yin hidima ga harkokin zirga-zirga a Beijing, wato ke nan za a kafa hanyoyin musamman domin taron wasannin Olympic, wadanda ba za su kawo cikas ga zaman yau da kullum na mazauna birnin ba.

A takaice dai, ayyukan shirye-shirye na gasar cin kofin duniya ta wasan softball da aka yi a wannan gami sun gamsar da hadaddiyar kungiyar wasan softball ta kasa da kasa da kuma karamar kungiyar sa ido ta kwamitin wasannin Olympic na kasa da kasa. Shugaban hadaddiyar kungiyar wasan softball ta kasa da kasa Mr. Don Porter ya fadi, cewa mun yi farin ciki matuka da kai ziyarar gani da ido a ayyukan gini na filaye da dakunan wasa, wadanda suka dace da bukatunmu sosai. ( Sani Wang )