Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-03-01 20:36:04    
Wani bayani dangane da Takaitaccen tarihi na majalisar ba da shawara kan harkokin siyasa ta kasar Sin (babi daya)

cri

Jama'a masu sauraro, yanzu ga shirinmu na "Me ka sani game da kasar Sin", a cikin shirinmu na yau za mu soma daga wani bayani dangane da Takaitaccen tarihi na majalisar ba da shawara kan harkokin siyasa ta kasar Sin .

An kafa Majalisar ba da shawara kan harkokin siyasa ta kasar Sin a ranar 21 ga watan Satumba na shekarar 1949.

Daga ranar 21 zuwa ranar 30 ga watan Satumba na shekarar 1949, an kira cikakken taro na farko na majalisar ba da shawara kan harkokin siyasa ta kasar Sin a birnin Beiping, wato birnin Beijing na yau ke nan, taron nan ya wakilci Majalisar wakilan jama'ar kasar Sin wajen aiwatar da harkokinta da kuma a madadin ra'ayin dukkan jama'ar kasar Sin ne ta shelanta cewa, Jamhuriyar Jama'ar Sin ta kafu. Taron ya zartas da "tsarin hadin kai na majalisar ba da shawara kan harkokin siyasa ta jama'ar kasar Sin wanda ya ke da halin tsarin mulkin kasa ta wucin gadi", sa'anan kuma taron ya zartas da "dokar tsara Majalisar ba da shawara kan harkokin siyasa ta kasar Sin" da "dokar tsara gwamnatin jama'a ta tsakiya ta Jamhuriyar Jama"ar Sin", an kuma tsai da cewa, birnin Beijing shi ne hedkwatar kasar Sin, kuma tutar kasa ita ce tuta mai launin ja da ke da sifar taurari guda biyar a kanta, taken kasa kuma shi ne "Kidan marchi masu sa kai", kuma an mayar da kalandar miladiyya bisa matsayin kalandar kasar Sin, an kuma zabi kwamitin tsakiya na gwamnatin jama'a ta Jamhuriyar jama'ar Sin da kwamitin farko na Majalisar ba da shawara kan harkokin siyasa ta kasar Sin. A ranar 2 ga watan Disamba na shekarar 1949, bisa shawarar da kwamitin majalisar ba da shawara kan harkokin siyasa ta duk kasar Sin ne, kwamitin gwamnatin tsakiya ya tsai da kudurin cewa, ranar 1 ga watan Oktoba ita ce ranar bikin kasa.

Bayan kafuwar Jamhuriyar Jama"ar Sin , Majalisar ba da shawara kan harkokin siyasa ta kasar Sin ta samar da gudumowa mai muhimmanci sosai ga farfado da tattalin arzikin kasa da raya shi da inganta sabon mulkin jama'a da ba da taimako ga gwamnati wajen sa kaimi ga yin kwaskwarima kan zamantakewar al'umma a fannoni daban daban da kuma sa kaimi ga yin juyin juya hali irin na gurguzu da raya kasa.

A watan Satumba na shekarar 1954, Majalisar ba da shawara kan harkokin siyasa ta farko ta kira zamanta na farko, inda ta zartas da tsarin mulkin kasa na Jamhuriyar Jama'ar Sin. A watan Disamba na wannan shekara, an kira taro na farko na Majalisar ta biyu, inda aka tsara babban tsarin Majalisar. Tsarin ya shelanta cewa, tsarin mulkin kasa ya riga ya maye gurbin tsarin tarayya, kuma hakkin da ke bisa wuyan cikakken zama na Majalisar ba da shawara kan harkokin siyasa ta jama'ar kasar Sin da ke wakiltar hakkin Majalisar wakilan jama'ar kasar Sin ya kammala ayyukanta, amma majalisar ba da shawara kan harkokin siyasa da ke bisa matsayin kungiyar fagen fama ta dimokuradiyar jama'a ta ci gaba da bayar da amfaninta mai muhimmanci sosai wajen hada kan jama'ar kabilu daban daban da kungiyoyi masu kishin kasa na rukunoni daban daban da yada dimokuradiyar jama'a da raya siyasar kasa da zamantakewar al'umma da kuma tayar da himmar dukkan abubuwa masu yakini don samar da hidima ga ayyukan raya kasa.

Game da gudanar da ayyukan raya kasa da Majalisar ta yi da ba a taba gani ba a cikin rabin karni, an iya takaita ta a kan manyan batutuwa guda biyu, wato hadin kai da dimokuradiya. A karkashin shugabancin Jam'iyyar Kwaminis ta Kasar Sin , yin hadin kai da dimokuradiya, hali ne mai muhimmanci ga Majalisar jama'a, kuma shaida ce ga tarihin haifar da Majalisar da raya ta, kuma manufa da dawainiya ne ga majalisar.

Shugabanta na yanzu shi ne Mr Jai Qinglin.

Sigar Majalisar da matsayinta Majalisar ita ce haddiyyar kungiyar fagen fama ta kishin kasa ta jama'ar kasar Sin, kuma muhimmiyar hukuma ce ta yin hadin guiwa da jam'iyyu da yawa da ba da shawara kan harkokin siyasa a karkashin Jam'iyyar Kwaminis ta Kasar Sin, sa'anan kuma hanya ce mai muhimmanci ta raya dimokuradiyar gurguzu a zamantakewar al'umma.

Babban tsarin siyasar kasar Sin shi ne, a karkashin jam'iyyar Kwaminis ta Kasar Sin, ana tafiyar da tsarin Majalisar wakilan jama'a da yin hadin kan jam'iyyu da yawa da tsarin Majalisar ba da shawara kan harkokin siyasa da tsarin aiwatar da harkokinsu na kansu a yankunan kananan kabilu. ( za a cigaba)