Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-03-01 15:14:23    
Ko za a sake yin gasar jan damara a tsakanin Rasha da Amurka?

cri

Kwanan baya, a lokacin da Amurka take kokarin kafa tsarin makamai masu kakkabo da makamai masu linzami a Turai, Rasha kuma ta sanar da cewa, za ta kara saurin bincike da kafa tsarin makamai masu linzami na sabon salo na 5. Duk wadannan aikace- aikacen da Rasha da Amurka suka yi wajen yin bincike da kafa tsarin makamai masu kakkabo da makamai masu linzami sun tunasar da mutane lokacin yakin cacar baki wanda kokawar da aka yi tsakanin Amurka da Rasha ke alamanta, kasashen duniya sun fara damuwa cewa, ko za a sake yin gasar jan damara a tsakanin Rasha da Amurka?

A shekaru na 50 zuwa karshen shekaru na 60 na karnin da ya wuce, an taba yin wata babbar gasar jan damara tsakanin Rasha da Amurka domin neman kafa tsarin makamai masu kakkabo da makamai masu linzami. A wancan lokaci kuwa, Rasha da Amurka sun yi kokarin bincike da kera makamai masu linzami, a sa'i daya kuma sun mai hankali sosai wajen bincike da kafa tsarin makamai masu kakkabo da makamai masu linzami.

Bisa halin haka, a shekarar 1972 an daddale "yarjejeniyar kayyade tsarin makamai masu kakkabo da makamai masu linzami" tsakanin Amurka da Rasha wadda aka dauke ta a matsayin harsashin samun zama mai dorewa na muhimman tsare-tsaren duniya, muhimmin abun da aka tanada cikin wannan yarjejeniya shi ne, za a samu tabbaci ga samun karfin hana barazana ya juna ta hanyar hana bangarorin 2 bunkasa tsarin makamai masu kakkabo da makamai masu linzami. Amma bayan hargitsin "ran 11 ga watan Satumba" wato a shekarar 2002, Amurka ta janye jikinta daga yarjejeniyar daga gefe guda kurum bisa dalilin yin yaki da ta'addanci, wannan kuwa dalilin da ya sa daga baya Amurka ta kafa tsarin makamai masu kakkabo da makamai masu linzami a yankunan kasar da na sauran kasashe.

Kwanan baya Rasha da Amurka sun yi ayyuka da yawa wajen bincike da kafa tsarin makamai masu kakkabo da makamai masu linzami, halin da ake ciki yanzu lalle ya yi kama da na shekaru 50 zuwa 60 na karnin da ya wuce.

Sabo da haka an ce, damuwar da kasashen duniya ke yi kan aikace-aikacen da kasashen 2 wato Rasha da Amurka ke yi wajen yin bincike da kera dimbin makamai masu kakkabo da makamai masu linzami tana da gaskiya. Amma idan an yi magana bisa ra'ayin hangen nesa, kusan a ce ba yiwuwar yin sabon gasar jan damara tsakanin Rasha da Amurka.

Dalilin da ya sa a ce haha shi ne, na farko, ba za a iya tauye halin daidaici wajen muhimman tsare-tsare na shiyya-shiyya cikin gajeren lokaci ba. Ko da yake Amurak ta yi ta habaka tsarin makamai masu kakkabo da makamai masu linzami har zuwa bakin kokar Rasha, amma har ila yau Rasha tana da isassun makamai masu fada domin maganin tsarin makamai na Amurka.

Na 2, yanzu Rasha da Amurka suna da moriyar tarayya a fannoni da yawa, sabo da haka bangarorin 2 sun yi matukar kokari domin kauce wa hargitsin da zai faru a tsakaninsu kai tsaye. A fannin yaki da ta'addanci, da hana yaduwar manyan makamai masu kare dangi, da matsalar Iran da ta Iraki da kuma matsalar nukiliya ta Korea ta arewa, Rasha da Amurka dukkansu suna da moriyar tarayya a kansu, kuma suna bukatar hadin gwiwa mai amfani a tsakaninsu.

Na 3, halin da ake ciki yanzu a kasashen duniya ya sha bamban da na lokacin yakin cacar baki. Gasar jan damara da aka yi a wancan zamani a tsakanin Amurka da Arasha ta faru ne bisa halin da "kasaitattun kasashe 2" wadanda suka yi kunnen doki, amma halin siyasa da ake ciki a duniya ta yanzu ya riga ya yi manyan sauye- sauye, wato yanzu ya kasance da "kasaitacciyar kasa daya da kasashe masu karfi da yawa" a duniya, babu harsashin sake yin gasar jan damara tsakanin Rasha da Amurka. (Umaru)