Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-02-28 21:40:54    
Kwararru suna magana kan ziyarar da Dick Cheney ya yi a Asiya da tekun Pasific

cri

Mataimakin shugaban kasar Amurka Dick Cheney ya yi ziyara a karshen kwanaki goma na watan Fabrairu a kasashen Asiya da tekun Pasific, inda bi da bi ne ya ziyarci kasar Japan da kasar Australiya da Amman da Pakistan da Afghannistan da sauransu. Ina dalilin da ya sa ya zabi wadannan kasashe don yin ziyara, kuma wane irin sakamakon da ya samu a gun ziyarar, kuma wane irin labarin da ya fayyace a gun ziyarar. Game da wadannan batutuwa, wani mataimakin shugaban kolejin koyar da ilmin dangantakar kasa da kasa ta jami'ar jama'a ta kasar Sin Mr Jin Canrong ya karbi ziyarar da wakilin gidan rediyo kasar Sin ya yi masa .A ganinsa, burin ziyarar da Mr Cheney ya yi a kasar Japan da kasar Australiya shi ne don sassauta damuwarsu a kan batun kasar Iraq da batun nukiliyar Korea ta Arewa da kuma ci gaba da neman goyon baya daga wajensu. Ya bayyana cewa, yanzu, a cikin kasar Amurka, ana sanya matsin janyewar sojoji daga kasar Iraq, kuma kasar Britaniya wadda ke zama abokiyarta sosai ita ma ta soma janye wasu sojojinta daga kasar Iraq, saboda haka kasar Amurka tana bukatar samun goyon baya daga wajen sauran 'yan kawancenta cikin gaggawa, makasudinta na farko shi ne don kara inganta huldar da ke tsakaninta da kasar Japan da kasar Australiya don samun wasu taimako wajen siyasa, game da batun nukiliyar Korea ta Arewa, shi ne batun da za a yi shawarwari a kai ta hanyar daidaituwa. Ana iya cewa, ziyarar ta sami nasara.

Amma abin da ba a taba tsammani a kai shi ne, a gun ziyarar Mr Cheney a kasar Japan da kasar Australiya, an yi abubuwan da suke shafar karfin soja na kasar Sin. A ranar 21 ga watan nan, lokacin da Mr Cheney ya yada zango na dan gajeren lokacin a kasar Japan, wani batun da ke cikin manyan batutuwan da ya yi shawarwari da firayim ministan kasar Japan Anbe shi ne, karfin da kasar Sin ta kara samuwa wajen harkokin soja da tasirinta da ke karuwa a duniya. A ranar 23 ga wannan wata, lokacin da Mr Cheney ya kai ziyara a kasar Australiya, ya sake bayyana dmuwarsa a kan habakawar soja da kasar Sin ta kara yi, ya bayyana cewa, ayyukan da kasar Sin ta yi ba su dace da manufarta ta tasowar zaman lafiya ba, Game da wannan, Mr Jim Canrong ya bayyana cewa, Mr Cheney yana daya daga cikin mutane masu taurin kai a gwamnatin W.Bush, muna mayar da shi cikin rukunin masu tsatsauren ra'ayi na gargajiya, halinsu na musamman shi ne , mai da hankali sosai ga karfin da ake da su, musamman ma a kan karfin soja, saboda haka sun mai da hankulansu sosai ga karfin soja na kasar Sin, amma a gun ziyarar da ya yi, ya yi ta yin magana a kan batun nan, ba kamar yadda aiki na yau da kullum da yake yi ba, amma daga wani fanni daban da aka gani , an ce, ba abun mamaki ba ne, duk saboda 'yan kawancenta guda biyu suna kusanci kasar Sin, kuma suna rashin fahimtarsu a kan saurin bunkasuwar kasar Sin, shi ya sa dukkansu suna da ra'ayi daya a fannin, musamman ma kasar Japan da kasar Amurka sun fi kasar Austaliya mai da hankalinsu ga kasar Sin.

Mr Jin Canrong ya kara da cewa, mutanen kasar Amurka suna da ra'ayinsu na kansu da cewar wai kasar Amurka ita ce cibiyar duniya , a ganinta, dukkan ayyukan da ta yi daidai ne, saboda haka lokacin da ta ga karuwar karfin da kasar Sin ta samu, to abin damuwa ne gare ta, nan gaba mutanen kasar Sin za su iya ganin hakan da kasar Amurka ta yi a kullum, kada mutanen kasar Sin su lura da wannan.

Mr Cheney ya kuma kai ziyara a kasar Pakistan da Afghanistan. Mr Jin Canrong ya bayyana cewa, babban aiki da ke bisa wuyan gwamnatin W.Bush a halin yanzu yana kan kasar Iraq, saboda haka a kan batun Afghanistan, yana fatan kasar Pakistan da kasashen da ke cikin kungiyar Nato za su iya daukar nauyi da yawa bisa wuyansu.

Abin da ke jawo hankulan mutane shi ne, ba zato ba tsammani Mr Cheney ya kai ziyara a kasar Amman. Mr Jin Canrong ya bayyana cewa, kasar Amman na da muhimmanci sosai bisa manyan tsare-tsare, ya kamata a kara mai da hankali ga ziyarar da Mr Cheney ya yi.(Halima