Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-02-28 21:25:49    
Babbar Ganuwar Sin

cri

A wannan mako, za mu amsa wasu tambayoyi dangane da babbar ganuwa ta kasar Sin. A cikin wasikar da shugaba Bello Abubakar Malam Gero daga kungiyar masu sauraren rediyon kasar Sin ta jihar Sokoto, tarayyar Nijeriya, ya aiko mana, ya tambaye mu, a wace shekara aka soma gina babbar ganuwar kasar Sin wadda ake kira The Great Wall of China? Shekaru nawa ne aka yi ana gininta? Yaya tsawonta yake daga kasa zuwa sama da kuma farkonta zuwa karshenta? Sa'an nan malam Sulaiman Dirani Jigawa da ya fito daga jihar Jigawa, tarayyar Nijeriya, ya rubuto mana cewa, a wane lokaci aka fara gina babbar ganuwar Sin, kuma a lokacin wane sarki. To, don kara fadakar da masu sauraronmu a kan babbar ganuwar Sin, yanzu sai ku gyara zama ku sha wani bayani dangane da ganuwar.

Babbar ganuwa ta kasar Sin wani gaggarumin aiki ne da aka fi jimawa ana yinsa a nan kasar Sin domin tsaro, har ma a duk duniya baki daya. Tun daga karni na bakwai kafin haihuwar annabi Isa alaihissalam ne, aka fara gina wannan babbar ganuwa. Daga bisani, an yi shekaru har 2000 ana ta gina ta ba tare da tsayawa ba. Wannan babbar ganuwa kuwa, ta shimfidu ne a filaye masu yawa da ke arewacin kasar Sin da kuma tsakiyarta, kuma tsawonta ya kai mita 7 zuwa 8 daga kasa zuwa sama da kuma kilomita sama da dubu 50 daga farkonta zuwa karshenta gaba daya. Babban aiki irinta a kasar Sin ita kadai, ko a duk duniya ma ba za a iya samun wani daban ba. Sabo da haka, an sa ta cikin gaggaruman ayyuka 7 masu ban mamaki na duniya a shekaru daruruwa da suka gabata.

Muna iya bin asalin babbar ganuwar daga karni na 9 kafin haihuwar annabi Isa alaihissalam, wato a zamanin daular Xizhou na gargajiyar kasar Sin. A lokacin, daular Zhou ta gina wasu gine-gine a jere domin kin harin 'yan kabilun makiyaya daga arewa. Ya zuwa karni na bakwai kafin haihuwar annabi Isa, wato a zamanin Chunqiu da kuma zamanin yake-yaken dauloli, dauloli daban daban sun sha yin takara da juna don neman fadada ikonsu, kuma sun yi ta gina ganuwa a kan iyakarsu, domin tsaron kansu da kuma magance hari daga sauran dauloli. Amma ganuwar da aka gina a lokacin gajera ce, tsawonsu ya kai kilomita dubu zuwa dubu biyu ne kawai.

Daga baya kuma, a shekara ta 221 kafin haihuwar Annabi Isa, sarki Qinshihuang ya murkushe masarautan sauran dauloli shida, kuma ya harhada daulolin da su zama kasa daya a karkashin mulkinsa. Domin neman magance hari daga makiyaya 'yan kabilar Xiongnu da ke arewa, da kara inganta tsaron kasa da kuma kwanciyar hankali, sai ya habaka babbar ganuwar bisa tsoffin ganuwar da aka rigaya aka gina. Bayan sarki Qinshihuang, daulolin da suke jan ragamar mulki duk sai suka ci gaba da gyaran babbar ganuwar da kuma habaka ta. Musamman ma a zamanin daulolin Han da Jin da kuma Ming, babbar ganuwar ta fi kasaita, har ma tsawonta ya kai kilomita dubu 5 ko kuma dubu 10. Ma iya cewa, a cikin tsawon shekaru sama da 2000 tun daga zamanin Chunqiu da zamanin yake-yaken dauloli har zuwa zamanin daular Qing, an yi ta gina babbar ganuwar ba tare da tsayawa ba.

Babbar ganuwa ta kasar Sin wadda ke da tsawon kilomita dubu 50, ba wai kawai wata ganuwa ba ce, a'a, ita wani cikakken tsari ne na tsaro a zamanin gargajiya wanda ke kunshe da katangu da gine-ginen ba da alamar yaki da gine-ginen soja da dai sauran gine-gine na tsaro, kuma yana samun jagoranci ne daga tsarin sojoji na matakai daban daban.

Yau babbar ganuwar Sin ta zama wani mashahurin wuri da dole ne masu yawon shakatawa na gida da na waje su ziyarta, a shekara ta 1987, kungiyar UNESCO ta kuma sa ta cikin jerin shahararrun wuraren tarihi na duniya. Masu sauraro, idan wata rana kun sami damar zuwa nan kasar Sin, kada dai babbar ganuwa ta Sin ta wuce ku, sabo da Sinawa kan ce, "ba za ka iya zama namiji na sosai ba, idan ba ka hau kan babbar ganuwa ba."(Lubabatu)