Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-02-28 08:19:24    
Ayyukan wasannin motsa jiki da jama`a ke shirya don taya murnar bikin bazara na gargajiyar kasar Sin

cri

Masu sauraro,kamar yadda kuka sani,ran 18 ga wata ita ce bikin bazara na gargajiyar kasar Sin na wannan shekara.Bisa kalandar gargajiyar kasar Sin,sabuwar shekara ta fara ce daga wannan rana,kuma bikin nan shi ne biki mafi muhimmanci ga mutanen kasar Sin wato mutanen kasar Sin sun fi mai da hankali kan wannan biki a duk shekara.A cikin shirinmu na yau,bari mu yi muku bayani kan ayyukan wasannin motsa jiki da jama`ar kasar Sin ke shirya don taya murnar wannan gaggarumin biki.

A kasar Sin,ayyukan wasannin motsa jiki na jama`a suna da dogon tarihi,a hakika dai,ayyukan wasannin motsa jiki na jama`a suna nuna mana al`adun gargajiya na zaman rayuwar jama`ar kasar Sin.A kullum a shirya wadannan ayyuka yayin da ake taya murnar manyan bukukuwan kabilu daban daban na kasar Sin.Alal misali,a gun bikin share kaburbura na gargajiya na kasar Sin,mutane su kan tafi karkarar birane su hawa dutse a can kuma su yi wasa da shirwa;a gun bikin `Duanwu`,a kan yi wasan kwale-kwale cikin koguna;a gun bikin `Chongyang` wato bikin girmama tsofaffi,mutane su kan je hawa dutse domin hangen nesa.A gun bikin bazara kuwa,ayyukan da aka shirya sun fi yawa.

Da farko dai,bari mu yi muku bayani kan `wasan zoben bakin karfe`,irin wannan wasa ya yi yaduwa sosai a kudancin kasar Sin,kabilar Han da wasu kananan kabilun kasar Sin kamarsu kabilar Dong da ta Zhuang da ta Yao da ta Miao da sauransu sun fi son wasan.Bisa mataki na farko,alkalin wasa ya yi amfani da wata karamar igwa ya harbi wani zoben bakin karfe wanda aka daure da zane mai launuka biyar,daga baya kuma,`yan maza masu karfi sun fara yin takara domin neman samu wannan zobe bisa kungiya biyu,wato wadannan kungiyyoyi biyu sun yi gasa.Idan `dan wasa ya kai da wannan zobe zuwa wani wurin da aka tanada,to,kungiyarsa za ta ci nasara.A wurin wasa,`yan mata su kan sa tufafi masu kyan gani kuma su kan yi ihu domin sa kaimi ga mazan da suke zo.Shehu malami dake yin nazari kan wasannin motsa jiki na jama`ar kasar Sin na jami`ar kananan kabilun tsakiya ta kasar Sin Wei Xiaokang ya yi mana bayani cewa daga ka`idar gasa da aka tsara,ana iya cewa wasan zoben bakin karfe ya yi kama da wasan kwallon rugby na kasar Amerka,ya ce,  `Wasan zoben bakin karfe wasa ne na jarumai,ya yi kama da wasan kwallon rugby na kasar Amerka,muna kiransa da sunan wasan kwallon rugby na kasashen gabashin duniya.`

Amma yawan `yan wasan dake shiga wannan wasa a lokaci daya sun yi yawa sosai har su kan kai dari daya.`Yan wasa da `yan kallo suna jin dadi kwarai da gaske,shi ya sa wasan ya sami karbuwa sosai daga wajen jama`a.

Ban da wannan kuma,wani wasa mai sha`awa daban da jama`ar kasar Sin sun fi so shi ne wasan damisa.Wannan wasa ya fi yin suna saboda a wurare daban daban na kasashen duniya,a kullum sinawa su yi nune-nunen wasan damisa a gun bikin bazara na gargajiyar kasar Sin.A cikin sinima kuma ana iya kallon irin wannan wasa daga film na wasan karate wato `gongfu`.Shehu malami Wei Xiaokang ya ce,  `Game da wasan damisa,akwai wata tatsuniya.Mun ji an ce,a zamanin can can da,annoba mai tsanani ta yi yaduwa a kasar Sin,mutane da yawa sun mutu a sanadiyar haka,daga baya kuma wata dabba mai ban mamaki ta fito,sunanta shi ne `shekara`,idan `shekara` ta fito,sai annoba ta tafi cikin sauri.Saboda haka a lokacin hutu,mutanen kasar Sin su kan daure wani kaya da gora da zane mai launi bisa siffar `shekara` dake cikin zukatun mutane a yi wasa da shi tare da kide-kide don guje wa masifa.A kai a kai ne ana tsamani cewa `shekara` ta yi kama da damisa.`

Wasan dragon shi ma ya yi kama da wasan damisa,kamar yadda kowa ya sani,dragon shi ne alamar kabilar kasar Sin,shi ya sa mutanen kasar Sin su kan yi wasan dragon don taya murnar bikin bazara,wasan dragon shi ma yana da dogon tarihi har ya kai fiye da shekaru dubu biyu.Yanzu dai jama`ar kasar Sin su kan yi wasan fitilar dragon,shehu malami Wei Xiaokang ya ce,  `Wasan fitilar dragon shi ne wasan dragon tare da fitila,wato a sa fitila kan jikin kayan dragon da aka yi da gora da kuma zane mai launi,daga baya,a kada kan dragon don nuna fatan alheri na sabuwar shekara,a wannan lokaci,dole ne mutanen dake gabansa wato gaban kan dragon su yi wasan wuta domin nuna godiya.`

To,jama`a masu sauraro,karshen shirinmu na yau ke nan,ni Jamila da na gabatar nake cewa,ku zama lafiya,sai makon gobe war haka idan Allah ya kai mu.(Jamila Zhou)