Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-02-28 08:16:27    
Wasu labaru game da wasannin motsa jiki (21/02-27/02)

cri

Bisa kididdigar da hukumar kula da aikin sa kai ta kwamitin shirya taron wasannin Olimpic na birnin Beijing ta yi,an ce,ya zuwa farkon watan Fabrairu na shekarar bana,a birnin Beijing,gaba daya yawan mutanen da suka yi rajista domin zama masu sa kai na taron wasannin Olimpic na shekarar 2008 sun riga sun kai dubu 250,a sauran birane da jihohi na kasar Sin kuwa,yawansu su ma ya riga ya kai dubu 70.A cikinsu,malamai da dalibai na jami`o`in birnin Beijing wadanda suka yi rajista sun kai dubu 180,wato sun kai kashi 71 cikin dari.Game da wannan,Mr.Liu dake aiki a sashen share fage na hukumar kula da aikin sa kai na kwamitin shirya taron wasannin Olimpic na Beijing ya yi mana bayani cewa,yawan masu sa kai na zama na 29 na taron wasannin Olimpic da za a yi a kasar Sin za su fi yawa a tarihin wasannin Olimpic.Wato za a zabi masu sa kai dubu 100 musamman domin taron wasannin Olimpic na Beijing da taron wasannin Olimpic na nakasassu.

Ran 24 ga wata,a Hongkong,yankin musamman na kasar Sin,a hukunce ne aka fara gudanar da shirin masu sa kai na gasar tseren doki na taron wasannin Olimpic na shekarar 2008 da taron wasannin Olimpic na nakasassu.Masu sa kai wajen dari 2 wadanda za su fara aiki bisa mataki na farko sun halarci bikin da aka shirya a babban ginin wasannin Olimpic na Hongkong,Daga ran 2 zuwa ran 4 ga wata mai zuwa,za a fara horar da su,yawancinsu suna iya yaren Guangdong da sinanci da kuma turanci,kuma za su fara aiki a gun gasar gwaji ta tseren doki da za a yi a yanayin zafi na shekarar bana.

Ran 25 ga wata,agogon Beijing,an kammala zagaye na kusa da karshe na budaddiyar gasar kwallon tennis ta maza ta ABN a birnin Rotterdam na kasar Holand.A gun gasar da aka yi,`dan wasa daga kasar Crotia Ivan Ljubicic ya lashe `dan wasa daga kasar Rasha Davidenkov,ya samu iznin shiga zagaye na karshe na gasar nan.(Jamila Zhou)