A cikin shirinmu na yau, kamar yadda mu kan yi a da, da farko za mu karanta muku wasu abubuwa kan wani shahararren lambun da ke lardin Jiangxi na kasar Sin, daga baya kuma, za mu maimaita shirinmu na musamman na gasar kacici-kacici ta 'garin Panda, lardin Sichuan', za mu sake karanta muku bayanin musamman mai lakabi haka 'babban dutse na Qingchengshan da kuma madatsar ruwa ta Dujiangyan'.(music)
Lambun Qingyun na kusa da gadar Dingshan a bayan birnin Nanchang daga kudu a lardin Jiangxi. A zamanin daular Xihan, wato tun daga shekara ta 206 kafin haihuwar Annabi Isa A.S. zuwa ta 25 bayan haihuwar Annabi Isa A.S., Mei Fu, wanda ya taba zama gwamnan gundumar Nanchang, ya yi zama a nan bayan da ya yi ritaya, daga baya kuma ya gina wani gidan ibada na Meixian a wurin. A zamanin daular Dongjin, wani gwamna na gundumar Jingyang mai suna Xu Xun ya zo wannan wuri don shawo kan ambaliyar ruwa ta hanyar sarrafa ruwa. Ya canja sunan gidan ibada na Meixian zuwa na Taiji. A shekara ta 1661 bayan haihuwar Annabi Isa A. S., wato a farkon zamanin daular Qing, wani mashahurin mai zane wai shi Badashanren ya janye jikinsa daga harkokin zaman al'umma ya zo nan don yin zama a kebe, a lokacin nan an fara kiran wannan gidan ibada da suna 'Qingyun'. A shekara ta 1815 da ta gabata, an canja wannan suna zuwa gidan ibada na addinin Taoism na Qingyun.
An gina dakin tunawa da Badashanren a shekara ta 1959. Badashanren, wanda sunansa na gaskiya shi ne Zhu Da, shi ne daya daga cikin zuriyoyin sarki na farko na daular Ming wato Zhu Yuanzhang. Ya nuna gwanintarsa a fannonin tsara wakoki da bayanai. Rubutu da zane-zanen da ya yi sun nuna cikakken bambanci bisa na saura. Yanzu Badashanren ya taka muhimmiyar rawa a cikin tarihin fasahar zamani ta kasar Sin. An mayar da zane-zane da rubutu da sauran abubuwan fasaha da Badashanren ya yi tamkar dukiyar kasar Sin, sa'an nan kuma, masu zane-zane na gida da na waje suna jin dadin kallon wannan dukiya sosai.
|