Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-02-27 20:24:01    
Kara motsa jiki ga masu shan taba zai iya rage hadarin kamuwa da ciwon sankarar huhu

cri

Kowa ya sani, shan taba yana yin mumunar illa ga lafiyar jikin dan Adam, amma duk da haka, mutane masu dimbin yawa su kan shan taba. Ta wani sabon binciken da suka gudanar, kwararru masu aikin likitanci na kasar Amurka sun ba da shawarar cewa, ya kamata mutanen da ba su son yin watsi da shan taba da kuma wadanda ba su iya yin watsi da shan taba su kara motsa jiki, ta haka za su iya rage hadarin kamuwa da ciwon sankarar huhu.

Manazarta masu aikin likitanci na jami'ar Pennsylvania ta kasar Amurka sun buga wani rahoto a kan wata mujallar likitanci, cewa bayan da suka gudanar da bincike kan tsoffin mata masu shan taba, sun gano cewa, yiyuwar kamuwa da ciwon sankarar huhu ga masu shan taba da su kan motsa jiki ta ragu da kashi 35 cikin dari idan an kwatanta da wadanda ba su son motsa jiki. Amma Catherine Schmitz, mai kula da binciken ta jaddada cewa, ta sakamakon binciken da suka gudanar, kada a dauka cewa, wato idan aka kara motsa jiki, to za a iya shan taba ba tare da damuwa ba. Idan masu shan taba suna son rage hadarin kamuwa da ciwon sankarar huhu, muhimmin abu shi ne tsai da kudurin yin watsi da shan taba.

Manazarta sun yi amfani da kididdigar da aka samu ta binciken da aka gudanar kan lafiyar jikin mata a jihar Lowa ta kasar Amurka. Tun shekara ta 1986, aka fara gudanar da binciken ga tsoffin mata, kuma ya zuwa karshen shekara ta 2002, an samu labarun mata da yawansu ya zarce dubu 36, kuma 777 daga cikinsu sun kamu da ciwon sankarar huhu. Kuma an yi hasashen cewa, 125 daga cikin wadanda suka kamu da ciwon ba su shan taba ko kadan yayin da 177 daga cikinsu sun taba yin watsi da shan taba cikin nasara, ban da wannan kuma 475 daga cikinsu su kan shan taba har kullum. Haka kuma nazarin yana ganin cewa, wadanda suka fi saukin kamuwa da ciwon sankarar huhu su ne mutane masu shan taba kuma ba su son motsa jiki.

Bugu da kari kuma manazarta sun bayyana cewa, ya zuwa yanzu ba a san mene ne dalilin da ya sa yin motsa jiki ke iya rage yiyuwar kamuwa da ciwon sankarar huhu ba. Amma ana ganin cewa, mai yiyuwa ne sabo da yin motsa jiki ya iya kyautata aikin huhu, ta haka za a iya rage yawan kwayoyin sankara da ke cikin huhu.

Kwararre na farko a fannin kiwon lafiya na kungiyar kula da huhu ta kasar Amurka Norman Edelman ya bayyana cewa, yiyuwar kamuwa da ciwon sankarar huhu ga masu shan taba ta ninka sau 10 idan an kwatanta da marasa shan taba, shi ya sa bai kamata masu shan taba su dogara bisa yin motsa jiki wajen rage hadarin kamuwa da ciwon sankarar huhu ba.