Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-02-26 21:08:11    
Kasar Sin tana gaggauta kafa tsarin daidaita matsalolin da za su iya faruwa ba zato ba tsammani a birane

cri

Lokacin da gobara da girgizar kasa da ambaliyar ruwa da malalar tabo da kuma manyan cuttuttuka masu yaduwa da sauran bala'u suke faruwa, ko tsarin daidaita matsalolin ba zato na birane zai iya bayar da taimako ko a'a, wannan yana da nasaba da zaman lafiyar rayuwar jama'a da dukiyarsu. Sabo da haka, ko tsarin daidaita matsalolin da za su iya faruwa ba zato ba tsammani a wani birni yana da kyau ko a'a, wani ma'auni ne wajen tabbatar da bunkasuwar birnin. To, a cikin shirinmu na yau, za mu gabatar muku da bayani kan yadda kasar Sin ta kafa tsarin daidaita bala'o'in da za su iya faruwa ba zato ba tsammani a birane.

A lokacin bazara na shekara ta 2003, kasar Sin ta gamu da wata cuta mai yaduwa da ke da matukar tsanani wato cutar SARS, kuma a shekara ta 2005, cutar murur tsuntsaye ta bullo a wasu jihohin kasar Sin, haka kuma a shekara ta 2006, jihohin da ke kudancin kasar Sin sun gamu da mahaukaciyar guguwa a jere, dukkan wadannan bala'o'i sun jarraba karfin da kasar Sin take da shi na tinkarar aukuwar bala'o'I masu muni, haka kuma sun sa kaimi ga kyautatuwar tsarin daidaita bala'o'I na ba zata na biranen kasar Sin.

A shekara ta 2003, an taba samun barkewar matsananciyar cutar SARS a birnin Beijing. Masu gudanar da harkokin birnin sun fahimci cewa, rashin ci gaban tsarin daidaita bala'o'in ba zata ya kawo cikas ga masu kula da harkokin samun labarai cikin lokaci kan yanayin yaduwar annobar cutar, kuma wannan wani muhimmin dalili ne da ya sa cutar SARS ta samu yaduwa sosai a cikin gajerren lokaci. Ju Wensheng, shugaban cibiyar yada labarai ta hukumar kiwon lafiya ta birnin Beijing ya gaya wa wakilinmu cewa, a 'yan shekarun nan da suka gabata, an kara samun bunkasuwar tsarin daidaita matsalolin kiwon lafiya da za su iya faruwa ba zata ba tsammani a birnin Beijing. Kuma ya ce, "Gwamnatin birnin Beijing tana mai da hankali sosai kan bunkasuwar harkokin kiwon lafiyar jama'a, kuma ta gabatar da shawarar kara raya ayyukan kiwon lafiyar jama'a da kuma kafa ofisoshin musamman guda 13 da ke karkarshin jagorancinta, ciki har da ofishin kula da matsalolin kiwon lafiyar jama'a da za su iya faruwa ba zato ba tsammani. A waje daya kuma ma'aikatar kiwon lafiya ta kasar Sin ta bukaci wurare daban daban da su kafa irin wannan tsari."

Ya zuwa yanzu, yawan mutanen da ke zaune a birane da garuruwan kasar Sin ya kai kashi 40 cikin dari na dukkan yawan mutanen Sin, kuma jimlar kudade da kasar Sin ta samu daga birane wajen masana'antu ta kai kashi 50 cikin dari, yawan harajin da kasar Sin ta samu daga birane ya kai 80 cikin dari, haka kuma yawan mutane masu ilmi mai zurfi da masu aikin nazarin kimiyya da ke birane ya kai kashi 90 cikin dari. Sabo da haka muddin aka kafa tsarin shawo kan matsalolin da za su iya faruwa ba zato ba tsammani yadda ya kamata, to za a iya fuskantar bala'u daga indallahi da matsalolin kiwon lafiyar jama'a, ta yadda za a iya tabbatar da bunkasuwar birane. Amma mene ne kyakkyawan tsarin kula da irin wadannan matsaloli a birane? Fan Weicheng, daraktan muhimmin ofishin gwajin kashe gobara ta kimiyya na kasar Sin ya gaya mana cewa, "Tsarin daidaita matsalolin ba zatada ke iya faruwa a birane yana kunshe da abubuwa uku, wato wuraren ba da umurni ga shawo kan matsalolin ba zato, da muhimmin tsari na ba da taimako, da kuma tsarin manhaja na tsararriyar hanya."

Yanzu ana kafa irin wannan tsari a fannonin tsaron zaman lafiyar jama'a da zirga-zirga da kashe gobara da jiyya da samar da wutar lantarki da ruwa da kuma iskar gas a manyan birane daban daban na kasar Sin. Muddin al'amuran ba zata sun faru, to za a iya hada hukumomin da abin ya shafa tare don warware su ta yin amfani da tsarin shawo kan matsalolin ba zata.

Amma a waje daya kuma, kwararru sun nuna cewa, yanzu kasar Sin ta fi son kafa tsari iri daban daban don daidaita matsalolin ba zata. Alal misali, an kafa tsarin daidaita al'amuran ba zata da ke iya faruwa don wasannin Olympic, da tsarin ba da umurni wajen yaki da ta'addanci, da kuma tsarin daidaita matsalolin ba zata don cutar murar tsuntsaye, da dai sauransu. Amma idan sabbin matsaloli sun faru a birane, to wadannan tsare-tsare ba za su iya dacewa da sabon halin da ake ciki ba, sai dai a kara kago sabon tsari don daidaita sabbin matsololi, ta haka za a kara kudade masu dimbin yawa da ba a bukatar kashe su. Madam Wang Weiping, shugaba mai kula da fasaha ta kamfanin kafa tsare-tsare na NetGain na kasar Singapore da ke birnin Beijing ta bayyana cewa, "Ya kamata kasar Sin ta kafa wani tsarin bai daya wajen shawo kan matsalolin ba zata a birane. Dalilin da ya sa na fadi haka shi ne sabo da tsarin daidaita matsalolin ba zata yana da sarkakiya sosai, shi ya sa ake bukatar gudanar da shi domin samun sauki, haka kuma idan an kafa tsarin bai daya, za a iya yin amfani da shi cikin dogon lokaci." Kande Gao)