Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-02-26 21:05:30    
Takaitaccen bayani game da kabilar Li na kasar Sin

cri

Kabilar Li tana daya daga cikin kabilun da ke kudu da tsaunin Lingnan a kudancin kasar Sin. Yawancin 'yan kabilar suna zama a yankunan da ke kudu maso tsakiyar lardin Hannan. Sabo da suna zama a wurare daban daban, yare da harufa nasu suna da dan bambanci. Bisa kididdigar da aka yi a shekara ta 2000, yawan mutanen 'yan kabilar Li ya kai miliyan 1.24 da wani abu. Suna da yaren Li da harshen Sinanci. A shekarar 1957 ce aka kago harufan Li da bakakken boko.

Abubuwan tarihi da aka samu a lardin Hainan sun nuna cewa, yau kimanin shekaru dubu 5 da suka wuce, kakanin-kakanin kabilar Li ta yanzu sun riga sun zama, kuma sun fara sarar tsibirin Hainan, wato lardin Hainan na yanzu yake.

A da, muhimmiyar sana'ar kabilar Li ita ce aikin gona. Suna noman shinkafa da dankali da masara da dai sauransu. Suna kuma yin wasu sana'ar hannu da ta kama kifi da farauta da kiwon tsuntsaye da dabbobin gida da tsinci wasu 'ya'yan gandun daji domin zaman rayuwarsu ta yau da kullum.

Tun daga shekarar 1948, an fara yin gyare-gyare kan ikon mallakar gonaki ta hanyar dimokuradiyya a tsibirin Hainan. Sannan kuma, an raya masana'antu da aikin gona da zirga-zirga da na jigilar kayayyaki da sadarwa da ilmi da al'adu da harkokin kiwon lafiya a yankunan da 'yan kabilar Li suke zama. Musamman bayan da aka amince da tsibirin Hainan da ya zama wani lardi da wata unguwar musamman ta raya tattalin arziki wadda ta fi girma a kasar Sin, an kara saurin yin gyare-gyare da bude wa kasashen waje kofa a lardin Hainan. Tattalin arzikin yankunan kabilar Li yana kuma samun cigaba sosai. Zaman rayuwar jama'ar kabilar Li ma yana samun kyautatuwa.

Ko da yake a da kabilar Li ba ta da kalmomi da harufa, amma, sun kago adabin baki mai ni'ima da arziki ta hanyoyi iri iri ciki har da labaru da tatsuniyoyi da labarun yara da dai sauransu.

'Yan kabilar Li sun kware kan waka da rawa. Kide-kide da raye-raye nasu suna bayyana halin musamman na kabilar sosai.

Bisa al'adar kabilar Li, miji daya yana da mace daya a cikin kowane gidan kabilar. Bayan da yaransu suka girma, sai sun yi zama a wani gidan da aka gina su da ke dab da gidan iyayensu. Bugu da kari kuma, a cikin farkon shekaru 2 zuwa 8 bayan da aka yi aure, amariya ta kan ci gaba da zama tare da iyayenta. Ba a nuna bambanci ga yaran da aka haifa ba a sakamakon aure ba. Idan an kashe aure, ko mijinta ya mutu, mace tana da 'yancin sake neman aure. (Sanusi Chen)