Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-02-23 17:53:35    
Mene ne makomar maganar nukiliyar Iran

cri

An labarta ,cewa jiya Alhamis, babban daraktan hukumar makamashi ta kasa da kasa wato Mohammed Baradei ya gabatar da wani rahoto ga hukumar da kuma kwamitin sulhu na Majalisar Dinkin Duniya game da yadda gwamnatin Iran take aiwatar da kuduri mai lamba 1737 na kwamtin sulhun. Wannan rahoto ya tabbatar da, cewa kasar Iran ba ta cimma wa'adin kwanaki 60 da aka diba mata ba na dakatar da shirin inganta Uraniyun, wanda kuma ake ta takaddama a kai cikin dogon lokaci. Ra'ayoyin bainal jama'a sun yi hasashen cewa, bayan fitowar rahoton Mohammed Baradei, abubuwan da suka fi jawo hankulan mutane, su ne makomar maganar nukiliyar Iran ta yanzu da kuma karin matakai da al'ummar kasa da kasa za su dauka kan kasar Iran.

Rahoton da Mr. Baradei ya gabatar ya yi nuni da, cewa kawo yanzu dai gwamnatin Iran tana ci gaba da harhada na'urorin inganta sinadarin Uranium domin samun makamashin nukiliya. Ban da wannan kuma, rahoton ya bayyana cewa, saboda gaza samun hadin gwiwa daga bangaren Iran, don haka har ila yau dai sufitocin hukumar makamashi ta kasa da kasa ba su samu ci gaba wajen binciken shirin Iran na bunkasa nukiliya ba. Jim kadan bayan da Mohammed Baradei ya gabatar da wannan rahoto, sai mataimakin shugaban kungiyar makamashin nukiliya ta Iran wato Mohammed Saeidi ya sake nanata, cewa kasar Iran ta ki karbar tayin da aka kai mata na dakatar da inganta sinadarin Uranium wato ke nan za ta ci gaba da aiwatar da shirinta na bunkasa nukiliya. A lokaci daya kuma ya yi nuni da, cewa rahoton Baradei ya shaida cewa kasar Iran tana gudanar harkokin nukiliya ne ba domin sha'anin soja ba.

A nasa bangaren, babban sakataren majalisar dinkin duniya Mr. Ban Kimoon ya mayar da martani a ranar jiya kan ci gaban lamarin nukiliya na Iran, inda ya bayyana damuwa a kai yayin da yake kiran gwamnatin Iran da ta biya bukatun kwamitin sulhu na Majalisar da kuma farfado da shawarwari tare da al'ummar kasa da kasa, ta yadda za a daidaita wannan magana cikin lumana.

Jama'a masu sauraro, har zuwa yanzu dai, kasashen Yamma suna shakkun cewa gwamnatin Iran ta badda kama wajen yalwata makaman nukiliya a zahiri maimakon bunkasa fasahohin nukiliya domin jama'a. Amma daga nata bangaren, gwamnatin Iran tana tsayawa kan ra'ayinta cewa tana gudanar da shirin bunkasa nukiliya ne domin zaman lafiya kawai. Bisa ingizawar kasar Amurka da sauran kasashe ne, kwamitin sulhu na Majalisar Dinkin Duniya ya zartar da kuduri mai lamba 1737 a watan Disamba na shekarar bara,wanda ya bukaci gwamnatin Iran da ta dakatar da harkokin inganta sinadarin Uranium cikin kwanaki 60, amma Iran ba ta yi rangwame ba kafin wa'adin da aka diba mata ya cika

Ana ganin cewa, gwamnatin Iran ta yi dabaru biyu wajen fuskantar maganar nukiliya. Tun daga watan Disamba na shekarar bara, shugaban kasar Iran wato Mahmud Ahmedinajad yakan dauki ra'ayi mai tsauri a game da maganar nukiliya. A ran 21 ga wata, ya fadi cewa samun fasahohin bunkasa nukiliya yana da muhimmancin gaske ga kasar Iran, wadda kuma take kokarin samunsu daga dukkan fannoni a cikin dan gajeren lokaci. A wani fanni daban kuma, sauran manyan jami'an Iran sun bayyana sassaucin ra'ayi kan wannan magana, wato sun sha furta cewa kasar Iran tana so a daidaita wanann magana ta hanyar shawarwari kuma cikin lumana. Wannan dai ya shaida, cewa har yau dai kasar Iran ta fi son cin gajiya daga wanann lamari cikin yin amfani da dabarun biyu.

Wasu manazarta sun yi hasashen cewa, ko da yake Mr. Baradei ya gabatar da wanna rahoto, amma da kyar kwamitin sulhu zai tattauna maganar nukiliyar Iran nan da nan. Bisa shirin da aka tsara, an ce, hukumar makamashin kasa da kasa za ta tattauna rahoton Mr. Baradei a gun taron da majalisar hukumar za ta gudanar daga ran 5 zuwa ran 9 ga watan gobe ; An kuma kyautata zaton cewa, kwamitin sulhun zai tattauna maganar nan kafin a kawo karshen taron, inda zai saurari ra'ayoyi.

Al'ummar kasa da kasa suna fatan za a sake kawar da halin kiki-kaka game da maganar nukiliyar Iran. (Sani Wang )