Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-02-23 16:48:55    
Kungiyar wasan kwallon kafa ta mata ta kasar Sin na kokarin horaswa domin taron wasannin Olympic na Beijing

cri

Aminai makaunatai, ko kuna sane da cewa, kwanakin baya ba da dadewa ba, an gudanar da gasar wasan kwallon kafa na mata ta kasashe 4 ta Guangzhou ta shekarar 2007 a birnin Guangzhou dake kudancin kasar Sin. Kungiyar kasar jamus wadda take ita ce lambawan a duniya, da kungiyar kasar Amurka wadda take ita ce zakarar taron wasannin Olympic na Aden, da gogaggiyar kungiyar England a Turai da kuma kungiyar kasar Sin wato mai masaukin baki sun halarci wannan gasa. Game da kungiyar wasan kwallon kafa ta mata ta kasar Sin wadda ta yi baya-baya a 'yan shekarun da suka gabata, lallai gasar da aka gudanar a wannan gami ta kasance tamkar wani muhimmin aiki ne dake cikin ayyukan share fage da take yi ga halartar taron wasannin Olympic na Beijing a shekarar 2008.

Sanin kowa ne, kungiyar wasan kwallon kafa ta kasar Sin ta taba samun nasarori masu gamsarwa a tarihi, alal misali : ta taba samun lambar azurfa a gun gasar wasan kwallon kafa na mata ta taron wasannin Olympic na Atalanta a shekarar 1996 ; Ban da wannan kuma, ta yi alfaharin zama lambatu a gun gasar cin kofin duniya ta wasan kwallon kafa na mata a shekarar 1999. A fannin wasan kwallon kafa na mata, har kullum akan mayar da kungiyar kasar Sin a matsayin wata gogaggiyar kungiya da ake tsoronta bisa karfin da take da shi na buga kwallo. Amma a 'yan shekarun baya, kungiyar wasan kwallon kafa ta mata ta kasar Sin ta yi baya-baya saboda rashin samun sabon jini. Don haka, ta sha kaye sau da dama daga hannun gogaggun kasashen Jamus, da Amurka da dai sauransu na duniya. Ko a Asiya ma, ta sha kashi ba sau tari lokacin da ta kara da kungiyar Koriya ta Arewa wadda ta samu ci gaba da saurin gaske.

Kodayake kungiyar wasan kwallon kafa ta mata ta kasar Sin tana fuskantar mawuyacin yanayi, amma duk da haka, masu sha'awarta na kasar Sin suna yin bege sosai kan sakamakon a-zo-a-gani da za ta samu a gun taron wasannin Olympic na Beijing a shekarar 2008. To, bisa wannan hali dai, ko shakka babu 'yan kungiyar wasan kwallon kafa ta mata ta kasar Sin suna gamuwa da babban matsi. Lallai babu gudu babu ja da baya gare su, wato ke nan dole ne su haye wahalhalu don samun ci gaba cikin taka tsantsan. Game da wannan dai, tuni a shekarar 2004, hukumar kula da harkokin wasan kwallon kafa ta kasar Sin ta inganta horar da 'yan wasa mata samari da yara har ta samu sakamako mai kyau. A gun gasannin wasan kwallon kafa na samari mata na duniya da aka yi a shekarar 2004 da shekarar 2006, kungiyar kasar Sin ta samu lambatu. An riga an shigar da nagartattun 'yan wasa guda 10 na waannan kungiyoyi biyu cikin kungiyar kasa ta yanzu. Bullowar wadannan 'yan wasa ta samar da karfin ingizawa ga kungiyar kasar. A gun gasar kasashe 4 da aka yi a wannan gami a birnin Guangzhou, kungiyar kasar Sin dake hade da sabbin hannu da tsoffin hannu ta fid da gwani har ta lallasa kungiyar England da ci 2 da ba ko daya da kuma yin kunnen doki da kungiyar kasar Jamus wadda take kan matsayin farko a duniya yayin da ta sha kaye daga hannun kungiyar Amurka da ci 0 da 2. A karshe dai, ta zo ta 3 a gun gasar.

Bayan gasar, mai koyar da 'yan wasan kungiyar kasar Sin Mr. Wang Haiming ya fadi cewa, ta wannan gasa, kungiyar kasar Sin ta kara imanin samun maki mai kyau a gun taron wasannin Olympic na Beijing da kuma gano hanyar da za ta bi wajen samun bunkasuwa a nan gaba.

Jama'a masu sauraro, tun da aka soma gudanar da gasar kasashe 4 bisa gayyata, 'yan kungiyar wasan kwallon kafa na mata ta kasar Sin sun nuna kishin zuci wajen buga kwallo ; kuma abu mafi muhimmanci shi ne, wasu sabbin 'yan wasa na-gari sun fi nuna gwaninta a gun gasar. Game da wannan dai, Mr. Wang Haiming ya ce, an shigo da sabbin 'yan wasa cikin kungiyar kasar ne domin yin shiri sosai ga shiga gasar cin kofin duniya ta wasan kwallon kafa na mata da za a yi a wannan shekara da kuma taron wasannin Olympic na Beijing da za a yi a shekara mai zuwa.

Dukanin 'yan wasan kungiyar kasar Sin sun gane, cewa dole ne su kyautata fasahohi da kuma dabarun buga kwallo. Sun ce, a da, 'yan wasan gaba sukan yi kuskure wajen mika wa da kuma karbar kwallo ; wasu 'yan wasan baya ma ba su bada taimakon juna da kyau wajen tsaron gida ba. Wata sabuwar 'yar wasa mai suna Yue Min ta fadi, cewa manufar kungiyar kasar Sin kan aikin shiga taron wasannin Olympic ita ce, inganta aikin horaswa a fannin fasaha domin yin karo da kungiyoyin kasashen Turai da Amurka wadanda suka fi samun kyakkyawan ingancin jikuna a duniya.

Wassu kwararrun kasar Sin a fannin wasan kwallon kafa sun yi hasashen, cewa ya kamata kungiyar wasan kwallon kafa ta mata ta kasar Sin ta aiwatar da manufar nuna fasaha wajen buga kwallo, hakan zai iya cike gibin da suka samu a fannin tsawon jiki da kuma karfin buga kwallo, ta yadda kungiyar kasar Sin za ta kama muhimmin matsayi a dakalin wasan kwallon kafa na mata na duniya.( Sani Wang )