Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-02-23 16:42:32    
Kasar Sin tana mayar da kayayyaki da take yi da fata zaman matsayin kasa da kasa

cri

Tun daga wannan wata, kasar Sin ta fara manna tambari da Turanci kan kayayyakin da take yi da fata, sa'an nan kuma ta fara bayar da takardun shaidar sahihan kayayyakin fata da Turanci. Kwararru a fannin aikin fata na kasar Sin suna ganin cewa, fara manna tambarin sahihan kayayyakin fata da Turanci, zai kara kawo tasirin kayayyakin fata masu inganci da sauran kayayyakin fata na kasar Sin a kasuwannin kasa da kasa, kuma zai ba da taimako wajen mayar da kayayyakin da kasar Sin ke yi da fata zaman matsayin kasa da kasa. Malam Chen Zhanguang, mataimakin shugaban ofishin kula da tambarin sahihan kayayyakin fata na kungiyar hadin guiwar masana'antun yin kayayyakin fata ta kasar Sin ya bayyana cewa, sai da kayayyakin fata masu inganci ne sosai, za a ba su tambarin sahihan kayayyakin fata. Ya kara da cewa, "bisa matsayinta na wani bangare, kungiyar hadin guiwar masana'antun yin kayayyakin fata ta dauki alkawari ga masaya cewa, wajibi ne, duk kayayyaki da za su sami tambarin sahihan kayayyakin fata, da farko, sun dace da manyan sharuda uku kamar na daya, wajibi ne, duk kayayyaki da aka yi da fata iri na asali ne, na biyu, wajibi ne, duk kayayyakin fata kayayyaki ne masu inganci sosai. Na uku kuma wajibi ne, bayan da aka sayar da su, a yi musu hidima da kyau. "

A cikin 'yan shekarun nan da suka gabata, wasu masana'antun yin kayayyakin fata na kasar Sin sun fara gudanar da harkokinsu a kasuwannin kasa da kasa, sun sami kwarewa a wasu fannoni, kuma sun yi suna. Sabo da haka yanzu wadannan masana'antu suna bukatar samun taimako don mayar da masana'antun yin kayayyakin fata na kasar Sin zaman matsayin kasa da kasa. A cikin irin wannan hali ne, aka fara bayar da tambarin sahihan kayayyakin fata da Turanci.

Malam Su Chaoying, babban sakataren kungiyar hadin guiwar masana'antun yin kayayyakin fata ta kasar Sin ya bayyana makasudin yin amfani da tambarin sahihan kayayyakin fata da Turanci cewa, "makasudinsa shi ne domin gabatar da "sahihan kayayyakin fata" ga masaya na kasa da kasa ta hanyar samun amincewa daga wajen kungiyar hadin guiwar masana'antun yin kayayyakin. Yin amfani da "tambarin sahihan kayayyakin fata" zai sa kaimi ga aikin mayar da tambarin kayayyaki da kasar Sin ke yi da fata zama matsayin kasa da kasa."

An ruwaito cewa, kungiyar hadin guiwar masana'antun yin kayayyakin fata ta kasar Sin ta riga ta tsara shirin yin farfaganda a kan "tambarin sahihan kayayyakin fata" a jere. Da farko, a gun nunin kayayyakin fata na shiyyar Asiya da tekun Pacific da za a shirya a Hong Kong a watan Maris mai zuwa da nunin ulu da fata na kasa da kasa da za a shirya a birnin Moscow na kasar Rasha a tsakiyar shekarar bana, kasar Sin za ta gwada kayayyakin fata wadanda ke da tambarin sahihan kayayyakin fata da sauransu.

Malam Su Chaoying, babban sakataren kungiyar hadin guiwar masana'antun yin kayayyakin fata ta kasar Sin ya bayyana cewa, a bana, kungiyar za ta shugabanci masana'antun kasar Sin wajen shiga kasuwanni musamman na nahiyar Afrika. Ya ce, "kasuwannin Afrika bakon abu ne ga wasu masana'antun kasar Sin musamman kanana da matsakaitansu. Sabo da haka bisa matsayinta na kasar Sin, kungiyarmu tana sauke da nauyi da ke bisa wuyanta na shiga kasuwannin Afrika masu girma sosai. Ana taimakon juna a tsakaninmu da kasuwannin Afrika. Don haka kungiyarmu za ta dauki matakai masu yawa don jagorantar masana'antu wajen shiga kasuwannin Afrika. Ban da wannan kuma, a ganinmu, za mu shiga kasuwannin cikin sauki ta hanyar manna tambarin da Turanci, sa'an nan kuma za mu yi ciniki da 'yan kasuwa da masaya na Afrika cikin sauki."(Halilu)