Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-02-21 17:18:18    
Wasu labaru game da wasannin motsa jiki(15/02-21/02)

cri

Yau ma ga shi Allah ya sake hada mu a wannan shiri namu na wasannin motsa jiki, wanda mu kan gabatar muku ko wace ranar Laraba bayan labaru. A cikin shirinmu na yau, kamar yadda muka saba yi, da farko za mu karanta muku wasu labaru game da wasannin motsa jiki, daga baya kuma, sai wani bayanin musamman da ke cewa, 'yan wasan gudun kankara na gajeren zango na kasar Sin sun sami ci gaba saboda takarar da suka yi a tsakaninsu da takwarorinsu na kasar Korea ta Kudu.

A kwanan baya, kwamitin shirya taron wasannin Olympic na Beijing ya yi cikakken taro a karo na 4 a nan Beijing, inda shugaban kwamitin Mr. Liu Qi ya bayar da rahoto kan ayyukan shirya taron wasannin Olympic na Beijing. Mr. Liu ya jaddada cewa, shekara ta 2007 da muke ciki shekara ce mafi muhimmanci wajen shirya taron wasannin Olympic na Beijing, dukan birnin Beijing da kasar Sin za su yi namijin kokari wajen tabbatar da ganin cewa, an kusan kammala ayyukan shiryawa duka, ta haka za a dasa harsashi mai inganci wajen cin nasarar gudanarwa da taron wasannin Olympic na shekara ta 2008.

Ran 17 ga wata, an kawo karshen gasar ba da babbar kyauta ta wasan kwallon tebur da hadaddiyar kungiyar wasan kwallon tebur ta duniya ta shirya a kasar Qatar. A cikin gasa ta tsakanin namiji da namiji, dan wasa Ma Lin na kasar Sin ya zama zakara bayan da ya lashe abokin karawarsa Wang Liqin. A cikin gasa ta tsakanin mace da mace kuma, 'yar wasa Li Xiaoxia ta kasar Sin ta lashe abokiyar karawarta Wang Nan, ta haka ta zama zakara.

Ran 18 ga wata, a gun gasar wasan kwallon kafa ta duniya da aka yi bisa gayyata a yankin musamman na Hong Kong na kasar Sin, kungiyar wasan kwallon kafa ta maza ta kasar Sin ta lashe takwaranta ta kasar Australia da ci 2 da ba ko daya, wadanda shekarun dukan 'yan wasa na wadannan kasashe 2 bai kai 23 da haihuwa ba. Bisa ka'idojin da aka tsara, an ce, dole ne shekarun 'yan wasan da za su shiga gasannin wasan kwallon kafa ta taron wasannin Olympic bai kai 23 da haihuwa ba, kasashen Sin da Australia sun kafa wadannan kungiyoyi 2 ne domin share fage ga taron wasannin Olympic da za a yi a nan Beijing a shekara mai zuwa.(music)

Ran 17 ga wata, a gun gasar ba da babbar kyauta ta wasan iyo da aka yi a Missouri ta kasar Amurka, shahararren dan wasan iyo Michael Phelps na kasar Amurka ya karya matsayin bajimta na duniya da minti 1 da dakika 53 da motsi a cikin gasar iyon da ake kira 'Mallam-bude-littafi' mai tsawon mita 200 ta maza. Matsayin bajimta na duniya na da shi ne ya rike da shi.(Tasallah)