Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-02-21 17:16:57    
'Yan wasan gudun kankara na gajeren zango na kasar Sin sun sami ci gaba saboda takarar da aka yi

cri

An rufe taron wasannin motsa jiki na lokacin hunturu na Asiya a karo na 6 a birnin Changchun na kasar Sin a kwanan baya. A cikin gasanni masu zafi da 'yan wasan gudun kankara na gajeren zango suka yi a wannan karo, kungiyoyin kasashen Sin da Korea ta Kudu masu kwarewa sun raba dukan lambobin zinariya 8. Kungiyar kasar Sin ta ci babbar nasara a wannan karo, in an kwatanta da yadda ta yi a gun taron wasannin Olympic na lokacin hunturu na Torino na shekara ta 2006, a lokacin nan ta sami lambobin zinariya guda daya kawai, yayin da kungiyar kasar Korea ta Kudu ta sami guda 6.

Shugaban Hadaddiyar kungiyar wasan kankara ?a Asiya Zhang Myeng-syek, dan kasar Korea ta Kudu ya nuna babban yabo kan gasannin gudun kankara na gajeren zango da aka yi a wannan karo, yana ganin cewa, 'yan wasa sun kai matsayin duniya a cikin gasannin. Ya ce, 'A cikin kwanakin nan da suka wuce, kungiyoyin kasashen Sin da Korea ta Kudu sun yi takara mai zafi a tsakaninsu, ta haka kwarewar 'yan wasa ba kawai ta kai matsayi na Asiya ba, har ma ta kai matsayin duniya. Dukan kungiyoyin kasashen Sin da Korea ta Kudu sun zama kan gaba a duniya a fannin gasar gudun kankara na gajeren zango, saboda haka, gasar da aka yi a wannan karo sun yi kama da gasar fid da gwani ta wasan gudun kankara na gajeren zango ta duniya.'

Wasan gudun kankara na gajeren zango yana samun karbuwa sosai a shiyyar Gabashin Asiya, dukan kasashen Sin da Korea ta Kudu suna da kwararru da yawa, wadanda suka kai matsayi na duniya. A gun taron wasannin Olympic na birnin Salt Lake da na Torino, 'yan wasan kasar Sin mata sun zama zakaru a cikin gasar gudun kankara na gajeren zango na tsawon mita 500. Amma, saboda tsoffin 'yan wasan sun yi ritaya, kungiyar wasan gudun kankara na gajeren zango ta kasar Sin ta gamu da matsala a 'yan shekarun nan da suka wuce,

Duk da haka a cikin gasannin gudun kankara na gajeren zango da aka yi a Changchun, kungiyar kasar Sin ta nuna alamar farfadowa, ba kawai ta sami lambobin zinariya ba, har ma sabbin 'yan wasa sun kawo jiki, an kyautata halin da kungiyar kasar Sin ke ciki a fannin yin karancin sabbin 'yan wasa mata a shekarun baya da suka wuce. 'Yar wasa Wang Meng ta kasar Sin, wadda zakara ce a cikin gasar gudun kankara na gajeren zango na tsawon mita 500 a wannan karo, ta bayyana ra'ayinta kan yadda kungiyar mata ta kasar Sin ta nuna a gun wannan taron wasannin motsa jiki na lokacin hunturu, ta ce,

'A zahiri kuma, har kullum ina ganin cewa, ko da yake kungiyarmu ko kungiyar Korea ta Kudu ta sami lambobin zinariya 8, amma wannan bai shaida kome ba, na mai da hankali kan taron wasannin Olympic, shi ya sa za a iya ganin gibin da ke tsakanin kungiyarmu da kungiyar Korea ta Kudu a gun taron wasannin Olympic na lokacin hunturu na Vancouver na shekara ta 2010.'

Kungiyar maza ta kasar Sin ta fi ba mutane mamaki, ko da yake suna fuskantar 'yan wasan kasar Korea ta Kudu masu kwarewa, amma sabbin 'yan wasan kasar Sin sun sami lambobin zinariya 2. Abin farin ciki shi ne, sun ci irin wannan nasara ne ba kawai domin kwarewarsu ba, amma har ma domin taimakawa juna da 'yan wasan kasar Sin suka yi a cikin gasannin tsakanin kungiya kungiya. Dan wasan Sui Baoku na kasar Sin, wanda zakara ne a cikin gasa ta tsawon mita 1500, ya bayyana cewa, 'Yanzu mai yiwuwa ne yana kasancewa da gibi a tsakanin kungiyarmu da kungiyar kasar Korea ta Kudu a fannin kwarewa. A cikin gasanni iri 4 da aka yi a wannan karo, 'yan wasanmu maza mun zama zakaru a cikin gasanni 2. A gun taron wasannin Olympic da za a yi a shekara ta 2010, ina tsammani cewa, 'yan wasanmu maza za mu kwashe dukan lambobin zinariya.'

Ko da yake nasarori sun faranta rayukan mutane, amma cikin nitsuwa ne kungiyar kasar Sin ta gano cewa, an ba ta sauki ne a matsayin masaukin taron, a sa'i daya kuma, ta fuskanci abubuwan da aka gaza yi wajen fasaha.

'Yan wasan kungiyar gudun kankara na gajeren zango ta kasar Sin sun bayyana cewa, kungiyar Korea ta Kudu mai kwarewa 'yar takara ce da suke kokarin lashe ta, sun rika kyautata kwarewarsu a cikin takarar da ke tsakaninsu da 'yan wasan kasar Korea ta Kudu. A gaskiya kuma, saboda irin wannan takara ta sada zumunci da kuma yin koyi da juna a fannin fasaha, kungiyoyin kasashen Sin da Korea ta Kudu suna kan gaba a duk duniya a fannin gasar gudun kankara na gajeren zango, sun kuma samun ci gaba.(Tasallah)