Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-02-21 17:13:59    
Dandalin Tian'anmen

cri

Tambayar da za mu amsa a wannan mako ta fito ne daga hannun malam Shehu Na'allah Usman, mazaunin birnin Zaria na jihar Kaduna, tarayyar Nijeriya. A cikin wasikar da ya aiko mana, ya ce, ina fatan za ku ba ni tarihin asalin Tian'anmen Square, wato dandalin Tian'anmen. To, masu sauraro, yanzu sai ku gyara zama ku sha wani takaitaccen bayani dangane da dandalin Tian'anmen na kasar Sin wanda ya shahara har a duk fadin duniya.

Dandalin Tian'anmen yana cibiyar birnin Beijing, kuma tsawonsa ya kai mita 880 daga kudu zuwa arewa da kuma mita 500 daga gabas zuwa yamma, sa'an nan fadinsa ya kai muraba'in mita dubu 440. Dandalin yana iya daukar mutanen da yawansu ya kai miliyan daya. Sabo da haka, ya zamanto Dandalin da ya fi girma a tsakanin dandalin da ke birane daban daban na duk duniya baki daya.

Da ma, a zamanin daulolin sarakunan gargajiya na Ming da Qing, dandalin Tian'anmen wani dandali ne da ke waje da babbar kofar fadar sarakuna. Bayan da aka kafa jamhuriyar jama'ar Sin, an fadada dandalin, kuma an gina wani babban dutse na tunawa da mazajen jiya a cibiyar dandalin Tian'anmen. A wurin da ke yamma da dandalin kuma, an gina babban dakin taron jama'a. Sa'an nan, gidan nuna kayayyakin juyin juya hali na kasar Sin da kuma gidan nuna kayayyakin tarihi na kasar Sin suna zaune ne a gabas da shi. Bayan haka, an kuma gina dakin tunawa da marigayi Mao Zedong, wato tsohon shugaban kasar Sin, a kudancin dandalin. A arewacin dandalin kuma, shahararriyar kofar Tian'anmen wadda aka gina ta a shekara ta 1417 tana tsayawa.

Dandalin Tian'anmen ya gane ma idonsa yadda jama'ar kasar Sin suka yi fafutukar juyin juya hali a zamanin da. Daga juyin juya halin da ya barke a ran 4 ga watan Mayu na shekarar 1919, inda jama'ar kasar Sin suka sanar da yaki da mayaudara da kuma daular sarakunan gargajiya, har zuwa lokacin da marigayi Mao Zedong, tsohon shugaban kasar Sin ya sanar da kafuwar Jamhuriyar jama'ar Sin a ran 1 ga watan Oktoba na shekara ta 1949, ga shi kuma da manyan bukukuwan kasa da aka shirya a nan dandalin, dandalin Tian'anmen ya zama wurin da aka samu aukuwar dimbin manyan al'amuran siyasa da na tarihi, ya kuma gane ma idonsa yadda kasar Sin ta farfado daga halin koma baya.

Yau dandalin Tian'anmen ya riga ya zama wata alama ta sabuwar kasar Sin. A kan tambarin kasar Sin, akwai hoton kofar Tian'anmen, a kan kudin Sin ma, akwai hotonta, yara kanana suna iya rerawa "ina son kofar Tian'anmen ta birnin Beijing. Ko wane dan kasar Sin, duk inda yake, zai tuna da dandalin Tian'anmen idan an ambaci kasar Sin, kuma idan an tabo magana kan dandalin Tian'anmen, zai iya tunawa da kasar mahaifarsa.

Yanzu dandalin Tian'anmen ya zama wani wurin da masu yawon shakatawa ba za su iya wucewa ba a nan birnin Beijing. An ce, idan kana son zuwa dandalin Tian'anmen domin yawon shakatawa, ya fi kyau ka je da safe, ka yi ta yawo, ka yi ta tunani. Idan ka iya shiga kofar Tian'anmen, to, daga inda ka tsaya, za ka iya hangen dandalin Tian'anmen da kuma babban titin nan na Chang'an, wanda ya ratsa filin har ma birnin Beijing daga gabas zuwa yamma, kana iya ganin tsoffin gine-ginen da aka gina a shekaru darurruwa da suka wuce tare kuma da sabbin gine-gine na zamani, kana kuma iya ganin tantabarun da ke shawagi a sararin sama. An ce, dandalin Tian'anmen ya kan karbi masu yawon shakatawa kimanin dubu 100 a ko wace rana, kuma a ko wace rana da safe, mutane dubu dubai su kan yi kallon bikin daga tutar kasar Sin a dandalin Tian'anmen. Masu sauraro, wata rana idan kun sami damar zuwa nan kasar Sin, kada dai ku wuce dandalin Tian'anmen, a nan za ku iya ganin tarihin kasar Sin da kuma yadda take a zamanin yanzu.(Lubabatu)