Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-02-21 17:12:17    
Bikin nuna girmamawa ga murhu

cri

Ranar 10 ga watan Fabrairu na shekarar da muke ciki ita ce ranar 23 ga watan Disamba na kalandar gargajiya ta manoman kasar Sin. Bisa al'adar kasar Sin, ranar nan rana ce ta nuna girmamawa ga murhu. Daga ranar nan , kasar Sin ta soma shiga gaggarumin bikin yanayin bazara na gargajiyarta.

Daga cikin dukkan aljannu na gargajiyar kasar Sin, aljannar murhu tana daya daga cikin dukkan tsofaffin aljannu na kasar Sin, tun daga ranar kafin shekaru dubu 2 da suka wuce, mutanen kasar Sin sun soma shirya bikin nuna girmamawa ga murhu.

An yada cewa, sarkin murhu shi ne aljannar wutar murhu da sarkin sararin samaniya ya nada, aikinsa shi ne aikin kula da harkokin murhu na iyalai daban daban, kuma ta sa ido ga ayyukan da dukkan mutanen iyalai daban daban suka yi a kodayaushe, an kuma mayar da shi bisa matsayin aljannun kare lafiyar mutane, saboda haka ya sami girmamawa sosai daga wajen mutane. A da, a cikin kowane dakin dafa abinci , an kafa abin nuna girmamawa ga aljannar murhu da kuma manna hoton aljannar murhu, a wurin da ke kan hoton nan, an kuma manna wata takardar da aka rubuta kalmomin da cewar wai " aljannar sa ido ga mutane ko sarkin dukkan iyali" , a gefunan biyu na hoton, an manna takardun da aka rubuta kalmomi wato Chunlian da cewar wai "hawa kan sararin samaniya don bayyana maganganu masu kyau kan al'amura masu kyau da aka yi, shiga cikin mutane don kiyaye lafiyarsu", duk saboda an bayyana cewa, a lokacin kusan karshen shekara, aljannar murhu zai hawa zuwa sararin samaniya don bayyana wa sarkin sararin samaniya dukkan abubuwa masu kyau ko masara kyau da dukkan mutanen iyalin nan suka yi a duk shekarar, bisa rahoton da aljannar ta yi ne, sarkin sararin samaniya zai tsai da kudurin samar wa dukkan mutanen iyalin nan zaman alheri ko masifa. Ranar tashi zuwa sararin samaniya da aljannar murhu ta yi ita ce ranar 23 ga watan Disamba ta kalandar gargajiya ta manoman kasar Sin, saboda haka mutanen kasar Sin sun shirya bikin nuna girmamawa ga aljannar murhu.

A maraicen ranar nuna girmamawa ga aljannar murfu, dukkan mutanen iyali sun taru gu daya cikin dakin dafa abinci wato kitchen ke nan, mai gidan ya shirya abinci iri iri a gaban hoton aljannar murfu, sa'anan ya yi addu'a da kuma kone turare. A cikin abincin da aka shirya, bai kamata ba a rasa wani abincin da ake kiran shi da cewar wai "Tanggua", wato wani irin alewa mai yauki sosai. Mun ji cewa, aljannar murhu ya fi son cin irin alewa, amma saboda irin alewa na da yauki sosai, shi ya sa ya kan lika bakin aljannar murhu sosai, kuma a wani lokaci bai iya yin magana ba, to ba zai iya yin maganganu masara kyau dangane da mutanen iyalinsa ga sarkin sararin samaniya ba. Bayan bikin da aka yi, sai mai gidan ya ciri hoton aljannar murfu, ya sanya shi a cikin murhu don konewa, sai aljannar murfu ya hawa zuwa sararin samiya ta hanyar fitar da hayakin murfu , ya zuwa jajibirin sabuwar shekara, sai mutane sun soma shirya bikin maraba da aljannar murfu, sun sake manna sabon hoton aljannar murfu, sai aljannar murhu ya sake komowa a tsakanin mutane, kuma ya ci gaba da kiyaye lafiyar dukkan mutanen iyalin da kuma sa ido ga aikace-aikacen da suke yi na yau da kullum.

A tsakanin mutanen kasar Sin, ana da karin magana cewa, ranar 23, alewa na da yauki sosai, ranar 24, ana shara sosai, ranar 25, ana dafa wani abincin da ake kiransa da cewa "Doufu", ranar 26, ana je sayen nama, ranar 27, ana kashe kaji, ranar 28, ana dafa wani irin abinci ta hanyar yin amfani da garin alkama tare da yis, ranar 29 , ana je sayen abin sha, ranar 30, ana dafa abinci na irin gargajiyar kasar Sin wato "Jiaozi", kai, kafin sabuwar shekara, ayyuka da yawa gare su. Amma dukkan ayyukan da mutanen suka yi ne bisa tsohuwar al'ada , yanzu , sai a kauyukan kasar Sin ana yin haka, a birane, yawancin iyalai ba su manna hotunan aljannar murfu da kuma yin bikin nuna girmamawa ga aljannar murhu ba, amma a cikin zuciyar mutane, in ranar 23 ga watan Disamba na kalandar gargajiyar kasar Sin ta zo, to bikin sabuwar shekara ya soma zuwa, a ko'ina a kauyuka da birane, ana shara sosai, ana farin ciki sosai, kuma ana kai da kawowa don sayi abinci iri iri da sauran abubuwa domin maraba da sabuwar shekara, wadanda suke aiki a wuraren da ke waje da gidansu suna soma komawa gidajensu don murnar bikin sabuwar shekara, wato bikin yanayin bazara.(Halima)