Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-02-20 17:48:27    
Yin yawo a cikin kungurmin daji ya fi kwantar da hankulan mutane

cri

Da farko, za mu gabatar muku da wani labari dangane da kiwon lafiya, bayan haka kuma, za mu gabatar muku da wani bayanin musamman da wakilin gidan Rediyon kasar Sin ya taho da shi, kan bayanin nan shi ne 'kasar Sin tana taimakwa yaran kauyuka da su yi karatu ba tare da biyan kudi da waya ba'.

Yanzu za mu soma gabatar muku da labarin da muka shirya muku game da yin yawo a cikin kungurmin daji. Da ma ana ganin cewa, yin yawo a cikin kungurmin daji na iya kwantar da hankali. Bayan da suka yi nazari, a kwanan baya masu nazari na kasar Japan sun sami shaida a fuskar kimiyya, sun tabbatar da cewa, yin yawo a cikin kungurmin daji yana iya kwantar da hankulan mutane.

Bisa labarin da jaridar 'Yomiuri Shimbun' ta kasar Japan ta bayar a 'yan kwanakin nan da suka wuce, an ce, masu nazari na cibiyar nazarin kungurmin daji ta kasar Japan sun zabi dalibai maza 12, sun yi yawo ko kuma hutu a cikin kungurmin daji, kashegari kuma, sun koma birane, daga baya, masu nazarin sun kwatanta adadin da suka samu daga jikunan wadannan dalibai a fannonin bugun zuciya da miyau da kuma hawan jini.

Sakamakon da suka samu ya nuna cewa, bayan da wadannan dalibai suka yi yawo ko kuma hutu a cikin kungurmin daji, sun fi kwantar da hankulansu, sun fi sassauta matsin lambar da suke fuskanta, haka kuma, an rage hawan jininsu. A takaice dai, yin yawo a cikin kungurmin daji yana da amfani mai ban mamaki.

Bisa wani labari daban da aka bayar, an ce, masu nazari na jami'ar ilmin likitanci ta ksar Japan su ma sun yi irin wannan jarabbawa. Sun zabi baligai 12 da su yi kwanaki 3 suna zama a cikin kungurmin daji, daga baya, an yi bincike kan jininsu. Sakamakon da aka samu ya yi nuni da cewa, bayan da suka yi zama a kungurmin daji, karfin garkuwar jiki na wadannan mutane 12 ya karu sosai.

Wani masani na cibiyar nazarin kungurmin daji ta kasar Japan yana ganin cewa, idan kungurmin daji yana da girma sosai, kuma akwai itatuwa da tsuntsaye da tsutsotsi iri daban daban a ciki, to, mutane za su kara kwantar da hankulansu, a lokacin da suke yin yawo ko kuma hutu a ciki.(Tasallah)