Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-02-20 17:44:35    
Dakunan shan shayi masu ban sha'awa a Tianjin

cri

Tabbas ne dakunan shan shayi manya da kanana da ke birnin Tianjin su burge mutanen da suka taba kai wa Tianjin ziyara. An mayar da birnin Tianjin tamkar garin wake-wake da kide-kiden gargajiya na kasar Sin da ke arewacin kasar Sin. Dakunan shan shayi sun fi nuna wannan sigar musamman ta Tianjin. A lokacin hutu, 'yan birnin Tianjin da yawa, musamman ma matasa, su kan je dakunan shan shayi, inda suke shan shayi tare da sauraren wasan 'yan kama mai ban dariya da kuma wake-waken da aka rera tare da ganga. Saboda haka, mutane daga wurare daban daban na kasar Sin su kan bakunci dakunan shan shayi a birnin Tianjin. Malam Ke Qiu, wanda ya zo daga birnin Wenzhou na lardin Zhejiang na kasar Sin, ya bayyana cewa,

'Na zo Tianjin a shekara ta 2002, a farkon lokacin da nake zama a Tianjin, ya kasance ba na yin kome a karshen mako, wani abokina ya fara ja na zuwa kallon wasan 'yan kama mai ban dariya a nan, na ji farin ciki. Sa'an nan kuma, na koyi wasu jimlolin yaren Tianjin, wadanda ke da sha'awa sosai a gare ni, kuma suna da ban dariya, a cikin sauran birane, ba na tsammani cewa, mutane sun yi magana ta irin wannan hanya mai ban dariya. A cikin shekaru baya da suka wuce, na kan gayyaci abokai da 'yan garinmu da abokan karatuna da ziyarce ni da su saurari wasan 'yan kama mai ban dariya, dukansu sun ji farin ciki bayan sauraren irin wannan wasa na Tianjin.'

Dakin shan shayi na Qian Xiang Yi da ke titin Guyi na unguwar Nankai ta Tianjin wani kanti ne da aka yi shekaru misalin 80 ana sayar da yadin siliki a da, amma an yi masa kwaskwarima, yanzu cike yake da sigogin gargajiya. Shan shayi da zama a kan kujera da kuma sauraren wake-wake da kide-kiden gargajiya na kasar Sin masu ban sha'awa dukansu suna bukatar ko wane mutum da ya kashe kudin Sin yuan 10 kawai. Idan an kashe kudi kadan, za a iya kece raini a nan. Shi ya sa a karshen ko wane mako, ko da yaushe mutane su kan cika dakin shan shayi na Qian Xiang Yi, kuma dariya ta cika dakin shan shayin, har ma ba a iya katse ta ba.

Jama'a masu sauraro, birnin Tianjin wani tsohon birni ne da ke da tarihi na tsawon shekaru misalin 600, shi kuma muhimmin birni ne na kasar Sin, inda aka gina tashoshin jiragen ruwa a birnin. Bunkasuwar zirga-zirga kan ruwa ta kawo wa birnin Tianjin al'adun kwata na musamman. Rukunoni daban daban na zamantakewar al'umma sun fito da yanayin al'adu iri daban daban, sa'an nan kuma, makomar mutane iri daban daban da kuma labarunsu sun samar da abubuwa da yawa wajen tsara wake-wake da kide-kiden gargajiya na kasar Sin a wannan birni, ta haka fasahar wake-wake da kide-kiden gargajiya na kasar Sin ta sami bunkasuwa sosai a birnin Tianjin. Har zuwa yanzu, a cikin dakunan shan shayi a nan, mutane na iya sauraren tsantsar wasan 'yan kama mai ban dariya na gargajiya. Darektan kamfanin yawon shakatawa mai suna 'kyakkyawan lokacin hutu' na Tianjin Chang Zhipeng ya bayyana cewa,

'A Beijing, akwai tsofaffin wuraren shakatawa na masarautun kasar Sin da aka gina a zamanin daular Ming da ta Qing, da kuma wasan kwaikwayo na waka irin na Beijing wato Beijing Opera. A biranen Suzhou da Hangzhou mutane su kan iya more idanunsu da kyawawan wurare masu ni'ima da sauraren wake-waken gargajiya na biranen. A garinmu na Tianjin kuwa, mutane na iya kallon wasu gine-gine masu dogon tarihi da fasahar gargajiya. Amma wake-wake da kide-kiden gargajiya na kasar Sin sun fi dadin ji, sun fi burge masu yawon shakatawa. A cikinsu kuma, wasan 'yan kama mai ban dariya ya fi saukin fahimta, kuma abubuwan da aka tanada a cikinsu su kan faranta wa mutane rayuwa sosai. Ana iya sauraren wasan 'yan kama a nan, har ma ana iya fahimtar sigogin gargajiya na wadannan dakunan shan shayi. Masu nuna wasan 'yan kama su kan bayyana tarihin Tianjin da sauye-sauyen da Tianjin ya samu da kuma labarun 'yan birnin ta hanya mai ban dariya, wannan ya fi bayanan da masu jagorancin yawon shakatawa suka yi kyau sosai.'

A wurare da yawa na Tianjin, a kan yi wake-wake da kide-kiden gargajiyar kasar Sin masu ban sha'awa a ko wace rana. Ci gaban zaman al'ummar kasa ya yamutse hanyoyin shakatawa da mutane ke bi, amma yanar giza gizo wato internet da bidiyo ba su iya maye gurbin wake-wake da kide-kiden gargajiya na kasar Sin da aka nuna kai tsaye ba. Sauraren wadannan wake-wake da kide-kiden gargajiya ba ma kawai yana bai wa mutane dariya ba, a sa'i daya kuma, yana sanya su kara fahimtar kan al'adun gargajiya na Tianjin da kuma halin da ake ciki a can.(Tasallah)