Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-02-20 17:42:45    
Wurin 'yan yawon shakatawa na al'adu na Nanshan

cri

A cikin shirinmu na yau, da farko za mu bayyana muku wasu abubuwa a kan wurin 'yan yawon shakatawa na al'adu na Nanshan, daga bisani kuma za mu karanta muku wani bayanin da ke cewa, ziyarar kwarin Jiuzhaigou da kuma wurin shakatawa na Huanglong ya yi kamar yadda kai ziyara ga Aljannar da ke duniyarmu, za mu maimaita shirinmu na musamman na gasar kacici-kacici ta 'garin Panda, lardin Sichuan'.

Wurin 'yan yawon shakatawa na al'adu na Nanshan ya zauna a yammacin birnin Sanya na lardin Hainan na kasar Sin. Fadinsa ya kai misaln murabba'in kilomita 50, a ciki kuma, akwai wani teku mai fadin misalin murabba'in kilomita 10.

Tun daga shekara ta 1998 har zuwa yanzu, mutane na gida da na waje miliyoyi sun yi ta ziyarar wurin 'yan yawon shakatawa na al'adu na Nanshan. An taba shirya kasaitattun harkoki da yawa a nan, wadanda suka hada da bikin harkokin neman samun tsawon rai na Nanshan da kuma bikin yawon shakatawa na Hainan da kuma bikin murnar zuwan sabbin shakaru 1000. Ban da wannan kuma, wurin shakatawa na al'adun addinin Buddha na Nanshan da wurin shakatawa na birnin Sanya da babban mutum-mutumin Avalokitesvara, wadda ake bauta mata saboda ta kan bai wa mutane tausayi da kuma kwalabar tawada ta dutse mafi girma a duniya su ma su kan jawo hankulan mutane.

Nanshan wuri ne mai muhimmanci sosai a cikin tarihin addinan Buddha da Taoism na kasar Sin. An ce, shahararren mai bin addinin Buddha Jian Zhen ya taba shan kaye a kan hanyarsa ta zuwa kasar Japan don yada addinin Buddha har sau 5, ya sake ci tura a farkon zuwansa na karo na 6, ya yi gantali zuwa Nanshan, a karshe dai ya cika burinsa ya isa kasar Japan bayan shekara guda da rabi.

Saboda ganin muhimmancinsa, an fara gina wurin shakatawa na al'adun addinin Buddha na Nanshan tun daga watan Nuwamba na shekara ta 1995, an kammala gina shi a watan Afril na shekara ta 1998. An kuma gina wani gidan ibada na Buddha a cikinsa, wanda ya fi girma bayan kafuwar sabuwar kasar Sin.(Tasallah)