Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-02-19 20:23:28    
Manufar yin gyare-gyare da bude kofa ga kasashen waje ta kyautata zaman rayuwar jama'ar Sin

cri
Kwanan nan ya kasance da bikin mafi muhimmanci ga Sinnawa wato bikin bazara, wato bikin sabuwar shekara na kalandar gargajiya ta kasar Sin. Cikin wadannan kwanaki masu murna da farin ciki, Sinawa da yawa sukan hada zaman jin dadin na yanzu da wata kalma wato "yin gyare-gyare da bude kofa ga kasashen waje". Daidai sabili da gyare-gyare da bude kofa ga kasashen waje da aka yi kasar Sin ne, shi ya sa Sinawa sun kubutar da kansu daga zaman talauci, kuma sun fara yin zaman wadata, kuma daidai sabili da manufar yin gyare-gyare da bude kofa ga kasashen waje da ake gudanar da ita a kasar Sin, shi ya sa kasar Sin ta bude kofarta da aka rufe cikin shekaru da yawa, kuma tana ta hada kanta da kasashen duniya a kwana a tashi:

Kwanan nan a wurare daban-daban na kasar Sin, ko a tsoffin kantuna masu dogon tarihi, ko ma a manyan katuna na zamani, dukkansu suna cike da mutane masu sayen kayayyaki domin murnar bikin bazara. A kan shahararen titin kasuwanci na Beijing wato babban titin Wangfujing, Mr. Yan Zixiang, dan birnin mai shekaru 27 da haihuwa yana nan yana sayen akwatin talbijin cikin wani kantin sayar da kayayyakin gida masu aiki da lantarki, ya ce, "A lokacin da nake da shekaru 6 zuwa 7 da haihuwa, gidanmu ya sayi wani akwatin talbijin mai girman inci 21, a wancan lokaci muna jin cewa irin wannan akwatin talbijin yana da kyau sosai. Amma kasuwar sayar da akwatunan talbijin ta samu ci gaba da saurin gaske, girman akwatun talbijin da ake sayarwa yanzu ya kai inci 29 har ma da inci 34, dukkansu kuma irin na zamani ne."

Daga shekarar 1978, kasar Sin ta fara gudanar da manufar yin gyare-gyare da bude kofa ga kasashen waje. Bisa jagorancin wannan manufar kuma tattalin arzikin kasar Sin ta samu bunkasuwa da saurin gaske. Yawan GDP wato jimlar kudin da aka samu daga aikin kawo albarkar kasa da aka samu ta karu daga fiye da dala biliyan 210 ta shekarar 1978 zuwa fiye da dala biliyan 2600 ta shekara bara, wato kasar Sin ta riga ta yalwatu ta zama babbar kasar tattalin arziki ta 4 cikin kasashen duniya. Jimlar kudaden da aka samu a shekarar 2006 wajen hajjojin da aka sayar a kasuwannin kasar Sin ta kai Renminbi wato kudin Sin fiye da Yuan biliyan 600, amma wannan ba abin zato ba ne yau da shekaru 30 da suka wuce.

Manufar yin gyare-gyare da bude kofa ga kasashen waje kuma ta kyautata zaman rayuwar jama'ar Sin wajen tunani. Barin mu dauki sinima kama da misali, yawan sinima da kasar Sin ta fitar a kowace shekara a tsakiyar shekaru 70 na karni na 20 bai kai 100 ba, amma zuwa shekara ta 2006 wannan adadi ya kai fiye da 300.

Ban da wannan kuma, manufar yin gyare-gyare da bude kofa ga kasashen waje da ake gudanar da ita a kasar Sin ta kara samar wa Sinawa da yawa da su samu damar zuwa kasashen waje don su gane ma idonsu kan abubuwan da suka faru a kasashen duniya. Zuwa karshen shekarar da ta wuce, yawan Sinawa da suka taba yin dalibci a kasashen waje ya wuce miliyan daya. Mr. Wang Huiyao shi ne mataimakin shugaban hadaddiyar kungiyar masu yin dalibci a kasashen waje ta kasar Sin ya taba yin dalibci a shekaru 80 na karnin da ya wuce a arewacin nahiyar Amurka, ya jiku kwarai ga manufar yin gyare-gyare da bude kofa ga kasashen waje da ake gudanar da ita a kasar Sin, ya ce, "Ina tsammani cewa, taimakon da Mr. Deng Xiaoping ya ba wa kasar Sin yana da girma sosai, ya kai kasar Sin zuwa wata kasa wadda kofarta bude take ga baki daga wata kasa wadda ada kofarta rufe take ga baki, wato ya kai kasar Sin zuwa cikin kasashen duniya. (Umaru)