Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-02-16 21:09:12    
Mr Abbas ya dora wa Haniyeh nauyin kafa sabuwar gwamnati

cri
Bayan da ta aiwatar da mulkin kasa a cikin watanni 11, sai gwamnati mai aiwatar da harkokinta na kanta ta Palesdinu da ke karkashin shugabancin kungiyar masu yin dagiya ta musulmi ta Palesdinu wato kungiyar Hamas ta yi shelar murabus cikin tarayya a ranar 15 ga wannan wata. Sa'anan kuma shugaban hukumar al'ummar Palesdinu Mr Mohmoud Abbas ya nada firayim ministan majalisar ministoci ta rikon kwarya Ismail Hamiyeh don ya dauki nauyi bisa wuyansa wajen kafa gwamnatin gamin gambiza ta Palesdinu. Wannan ya alamanta cewa, Palesdinu tana dora gaba bisa mataki mai muhimmanci wajen cim ma burin samun sulhuntawar al'umma da karya kangiyar tattalin arziki da aka yi mata a kasashen duniya.

A wannan rana, a Zirin Gaza, Mr Abbas ya shirya wani bikin nadawa a gajeren lokaci. A gun bikin, da farko, a madadin dukkan mambobin majalisar ministoci ne Mr Haniyeh ya gabatar wa Mr Abbas takardar murabus, bayan da Mr Abbas ya amince da takardar, sai ya nada Mr Haniyeh da ya kafa sabuwar gwamnati. Mr Abbas ya kuma kirayi sabuwar gwamnati da ta yi alkawarin ci gaba da aiwatar da kudurran kasashen duniya da aka tsai da dangane da Palesdinu da kuma yarjejeniyoyin da aka rattaba hannu a kansu a tsakanin kasar Isra'ila da Palesdinu. Mr Haniyeh ya kuma dauki alkawarin kafa sabuwar gwamnati bisa abubuwan da Mr Abbas ya tanada cikin takardar nadawa . Bisa dokokin shari'a na Palesdinu, Mr Haniyeh zai kammala kafa sabuwar gwamnati cikin makonni biyar masu zuwa, a duk tsawon lokacin, Mr Haniyeh zai ci gaba da daukar nauyin firayim ministan gwamnatin rikon kwarya.

Murabus da gwamnatin kungiyar Hamas ta yi da kuma nadawar da Mr Abbas ya yi wa Mr Haniyeh mataki ne mai muhimmanci da rukunoni daban daban na Palesdinu suka dauka a kan hanyar kafa gwamnatin gamin gambiza. A cikin shekarar da ta wuce, Palesdinu ta fada cikin rikici mai tsanani wajen harkokin kudi da hargitsin da ake yi cikin gidanta, kuma 'yunkurin kafa gwamnatin gamin gamibiza ya yi ta cin hasara. Bayan da kungiyar Hamas da ta Fatah suka yi shawarwari da haddasa rikici sosai a tsakaninsu a zagaye sau da yawa, a karshe dai sun soma aikin kafa sabuwar majalisar ministoci cikin hadin guiwa a hakika, wannan ya sa ran alheri ga kawo karshen hargitsin da ake yi a cikin gida da sake samun agajin tattalin arziki daga gamayyar kasa da kasa.

Amma kungiyar Hamas da kungiyar Fatah har wa yau dai suna fuskantar kalubale a fannoni da yawa.

Da farko, ya kamata a tabbatar da wadanda za su sami manyan mukamai a cikin sabuwar gwamnati. Bangarorin biyu har wa yau dai suna samun sabani a kan batun zaben mataimakin firayim minista da ministan harkokin gida da sauran manyan jami'ai.

Na biyu, Bangarorin biyu suna bukatar yin rangwame a kan batun daidaita dakarun kungiyar Hamas. Don yin adawa da rundunar tsaron kai ta Palesdinu da ke karkashin shugabancin kungiyar Fatah ne, kungiyar Hamas ta kafa wata rundunar soja ba bisa ka'ida ba kuma ba tare da kula da kiyewar da Mr Abbas ya yi ba. A ranar 15 ga wannan wata, Mr Haniyeh da Mr Abbas sun yi shawarwari a kan batun da abin ya shafa, amma ba su kawar sabanin da ke tsakaninsu ba.

Sa'anan kuma, Mr Abbas da Mr Haniyeh suna fuskantar matsin da kasashen waje suke yi musu game bukatar sabuwar gwamnati da ta amince da kasar Isra'ila da kuma yi shelar kawar da karfin tuwo da aka yi da kuma amince da dukkan yarjejeniyoyin da aka rattaba hannu a kansu a tsakanin Palesdinu da Isra'ila, in ba hakan ba, to kasar Amurka za ta ci gaba da yin adawa da gwamnatin, ba ta yi ma'amala da kowane mamban majalisar. Kasar Isra'ila ita ma ta karfafa cewa, kowace gwamnatin Palesdinu dole ne ta amincewa da sharudan nan guda uku na gamayyar kasa da kasa. Amma Mr Haniyeh da ke bisa matsayi mai muhimmanci a cikin gwamnatin rikon kwarya ya nace ga matsayinsa na rashin amincewa da kasar Isra'ila. Saboda haka abu ne mai wuya sosai da za a kawar da sabanin da ke tsakanin Mr Abbas da Mr Haniyeh.

A ranar 21 ga wannan wata, sakatariyar ma'aikatar harkokin waje ta kasar Amurka madam Condoleezza Rice za ta yi shawarwari da bangarori uku da ke hade da ita da Mr Abbas da firayim ministan kasar Isra'ila Ehud Olmert, matsayin siyasa na sabuwar gwamnatin Palesdinu zai zama batu mai muhimmanci a gun shawarwarin da za a yi.(Halima)