Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-02-15 15:53:11    
Majalisar dokokin Turai ta amince da rahoton bincike kan lamarin ' gidajen kurkuku na asiri'

cri

An labarta, cewa jiya Laraba, a birnin Strasbourg na kasar Faransa, cikakken zama na majalisar dokokin kasashen Turai ta yi na'am da rahoton bincike na karshe kan lamarin ' Gidajen kurkuku na asiri' dake shafar hukumar leken asiri ta Amurka wato C.I.A ; Rahoton ya tabbatar da, cewa tun daga shekarar 2001 zuwa shekarar 2005, jiragen sama da hukumar leken asiri ta Amurka ta yi amfani da su don jigilar mutanen da ake hukumarsu da laifin aikata ta'addanci sun taba tashi da sauka ko ketare sararin samaniya na wasu kasashen kungiyar tarayyar Turai, kuma kasar Amurka ta taba kafa gidajen kurkuku na asiri a Turai don tsare wadanda ake hukumars`u da laifin aikata ta'addanci.

Bayan da aka shafe shekara guda ana gudanar da bincike, sai kwamitin wucin gadi na majalisar dokokin Turai ya gabatar da wani daftarin tsari na rahoton bincike na karshe a ran 23 ga watan da ya gabata ; kuma a ran 14 ga watan da muke ciki, an yi kwaskwarimar wannan rahoto a wurare da dama, wanda kuma ya tabbatar da, cewa tun daga shekarar 2001 zuwa shekarar 2005, jiragen saman hukumar leken asiri ta kasar Amurka sun tashi da sauka ko ketare sararin samaniya a kalla sau 1,245 na kasashen kungiyar tarayyar Turai, kuma sau da yawa daga cikinsu sun shafi lamarin jigilar mutanen da ake tuhumarsu da laifin aikata ta'addanci. Sa'annan rahoton ya yi nuni da, cewa jiragen saman hukumar leken asiri ta Amurka sun sha tashi da sauka ko ratsa ta wasu kasashen Turai da suka hada da Jamus, da Burtaniya, da Ireland ,da Spain ,da Italiya, da Portugal, da Romania da kuma Poland da dai sauransu. Amma, kasashen Jamus da Burtaniya da kuma Italiya da dai sauransu sun gani sun kawar da fuska game da wannan lamari, hakan ya kauce wa dokokin shari'a da abun ya shafa na kasashen Turai.

Ban da wannan kuma rahoton ya yi suka kan wasu manyan jami'ai na kungiyar tarayyar Turai da kuma gwamnatocin kasashe mambobin kungiyar saboda ba su bada taimako ga binciken da kwamitin wucin gadi ya gudanar ba ; A lokaci daya kuma, ya bukaci hukumar koli ta kungiya tarayyar Turai wato majalisar kungiyar hadin kan Turai da ta gudanar da 'bincike mai zaman kai' idan abun ya zama wajaba ; Dadin dadawa, rahoton ya yi Allah wadai da hukumar leken asiri ta Amurka wato C.I.A saboda ta kafa gidajen kurkuku a sansanonin soja na kasar Amurka dake Turai domin tsare mutanen da ake tuhumarsu da laifin aikata ta'addanci yayin da yake yin kira ga gwamnatin Amurka da ta rufe gidan ayari dake sansanin tsare mutane dake Guantanamo na kasar Cuba.

Yanzu ana takaddama sosai kan wannan rahoton bincike a cikin majalisar dokokin Turai. Jam'iyyar Socialist Party ta bayyana ra'ayinta, cewa majalisa dokokin Turai tana gazawa wajen shawo kan sassan tsaro na Turai domin hukumomin leken asiri na kasar Amurka sun yi awon gaba da mutane sau da dama a Turai bayan aukuwar lama'in 'ran 11 ga Satumba'. Bisa wannan hali dai, ya kamata majalisar dokokin Turai ta ja kunnen kasashe daban daban na kungiyar tarayyar Turai don su sa lura sosai kan wannan lamarin keta hakkin bil adama ; Amma daga nasu bangaren, wasu jam'iyyu da rukunoni masu ra'ayin rikou sun yi hasashen cewa wai har yanzu ba a samu cikakkiyar shada game da binciken lamarin ' gidajen kurkuku na asiri' ba. Saboda haka ne suka hau kan kujerar-na-ki lokacin da ake jefa kuri'u don zartar da wannan rahoto.

Akwai alamu da yawa da suka shaida, cewa manyan hukumomi uku na kungiayr tarayyar Turai wato majalisar kungiyar, da kwamitin kungiyar da kuma majalisar dokokin Turai ba su hada kansu tamkar mutum daya kan wannan lamari ba. Ban da wannan kuma, wannan lamari yana shafar ra'ayin da wai sabbin kasashen Turai da kuma tsofaffin kasashen Turai suke daukawa kan kasar Amurka, da kuma magana mai yamutsu dake cewa ko kungiyar tarayyar Turai za ta kara hada kanta ko kuwa za ta kara samun bambancin ra'ayoyi.

Daidai bisa wadannan dalilai na siyasa ne, wasu manazarta suka fadi cewa da kyar kungiyar tarayyar Turai za ta gudanar da bincike na zahiri game da lamarin ' gidajen kurkuku na asiri'. ( Sani Wang )